19
Nov
Daga MAHDI M. MUHAMMAD An kwashi ’yan kallo a tsakanin ɗan wasan Super Eagles, Moses Simon, da fitaccen mataimakin kocin Nijeriya, Finidi George bayan Nijeriya ta sha kashi da ci 4-0 a hannun Portugal a wasan sada zumunci na ƙasa da ƙasa a daren Alhamis, 17 ga watan Nuwamba, 2022. Yayin da ’yan Najeriya ke ta takaicin rashin nasara a wasanni na sada zumunta a jere, mataimakin koci Finidi George da ɗan wasan gaba, Moses Simon sun aikata abin da ya ba kowa mamaki. A matsayin al'ada bayan wasan, 'yan wasa suna musayar riguna, abin da Moses da ɗan wasan…