Taiwo Awoniyi: Yadda birkila ɗan Nijeriya ya koma buga Firimiyar Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Lokacin da koci Steve Cooper ke ƙoƙarin gina harsashin Nottingham Forest don tsira a gasar firimiya, ya yi duban tsanaki inda ya ga ya dace ya ɗauko ɗan wasan farko wanda ya kasance tsohon mai aikin birkila.

Kuma tabbas Taiwo Awoniyi ya saka masa, yayin da ɗan Nijeriyar ya taimaka wurin nasarar da Forest ta samu na farko a kakar bara, wadda ta doke West Ham 1-0 da cin Arsenal 1-0, hakan ya sa ta ci gaba da zama a gasar Firimiya a watan Mayu.

Hakan ya zo ne saura mako ɗaya a ƙarƙare wasannin bara, inda Awoniyi ya zura ƙwallo a wasan ƙarshe inda da ya kawo ƙarshen cin ƙwallaye a kakar wasannin ta Forest ya kuma ba shi damar zura fiye da goma a gasar.

Hakan ya tabbatar da nasara a ƙarshen kakar wasan da Forest ta yi ta na neman tsira a gasar Firimiya, inda nasarorin da aka samu suka zo a makare, kamar yadda wasan Awoniyi ya kasance a ƙungiyar.

Ɗan wasan mai shekaru 25, wanda ya daɗe da burin buga wasa a gasar firimiyar Ingila tun yana ƙarami, ya jira har zuwa 2022 don buga gasar Firimiya ta farko duk da cewa ya qulla yarjejeniya da Liverpool shekaru bakwai a baya.

Rashin samun izinin aiki don yin wasa a Birtaniya shine babban dalilin hakan kuma koda yake ya zo a watan Mayu 2021, Liverpool ta sayar da Awoniyi bayan watanni biyu kacal.

A cikin shekaru shida da suka gabata, Reds ta bayar da aronsa sau bakwai.

Yayin da ya girma a Jihar Kwara a Nijeriya, Awoniyi ya kan shaida wa duk wanda ya ji cewa wata rana zai buga gasar Firimiya.

“Hakan ne kawai na cigaba da faɗa wa mutane kamar abokai na a makarantar sakandare da abokan wasa na, ko da mutane ba su yarda da abin da na fada a lokacin ba,” in ji shi.

“Daman haka na ke. Da zarar na yi imani da wani abu, sai na aiwatar da shi. Kuma zama ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa da buga gasar Firimiya shi ne babban burina.”

Daga farko a Nijeriya, ya kan karɓi ayyuka daban-daban, kamar yin aikin bulo ko ma kawai ɗebo ruwa ga makwabtansa don samun kuɗi, don biyan buqatun balaguron da ya yi, da kuma samun kuɗin tafiye-tafiye zu wajen atisaye, ko wajen sansanin da ake ɗaukar ɗan ƙwallo.

Duk da haka abubuwa ba su zo masa da sauƙi ba, inda wani lokaci ya kan sanya safa kusan nau’i goma don ya samu saka takalman da suka yi masa yawa ko kuma yin tafiya mai nisa a kafa don zuwa filin atisaye.

Har yanzu yana da kusanci da kocinsa na farko, Abdulrazaq Olojo, wanda sau da yawa ya kan ba Awoniyi kudi don zuwa wajen atisaye ko kuma ya rage masa hanya a kan babur ɗinsa, kuma bai taɓa mantawa cewa Seyi Olofinjana ya taimaka masa ba.

Tsohon ɗan wasan tsakiya na Wolverhampton Wanderers da Nijeriya ya gayyaci Awoniyi zuwa makarantarsa, wanda ya zura ƙwallaye huɗu a lokacin da Nijeriya ta lashe gasar cin kofin duniya na ‘yan ƙasa da shekaru 17 a 2013, kuma ya zama zakaran Afirka na ‘yan ƙasa da shekaru 20 bayan shekaru biyu, ya kuma koma Liverpool a 2015.

Olofinjana ya shaida wa manema labarai cewa, “Taiwo ya kasance ɗaya daga cikin matasan ‘yan wasa masu kwazo – har yanzu ya cigaba da yin fice,” Olofinjana ya shaida wa Sport Africa.

“A gare shi, abu ne kawai na lokaci – musamman saboda yadda ya riqe addini.”
Yana da zurfin addini, kuma Awoniyi ya na da ɗa’a, tare da mutunta asalinsa, kuma har yanzu yana hulɗa da waɗanda suka girma tare. Ya ce suna zaburar da shi kamar yadda shi ma ya ke zaburar da su.

Bayan ya koma Anfield, Awoniyi ya tafi aro a NEC Nijmegen ta Netherlands da Royal Excel Mouscron ta Belgium (sau biyu) da KAA Gent da kungiyoyin Jamus FSV Frankfurt da Mainz da Union Berlin don jawo hankalin masu zaven ‘yan wasan da ke buga wa kasa tamaula da kuma samun izinin aiki.

A shekarar 2021, kwalliya ta biya kuɗin sabulu a inda Awoniyi ya sami izinin aiki a Birtaniya, ya kuma buga cikakken wasansa na farko a Nijeriya, ya kuma sami komawa Union Berlin na dindindin don buga Bundesliga a Jamus.

A kakarsa ta farko da ya buga wa kulob ɗin Turai, Awoniyi ya zura qwallo 15 a gasar Bundesliga inda ya ja hankalin Cooper, wanda a lokacin ya sanya shi ya zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin Forest a watan Yunin bara.

Mai yiwuwa ya ɗauki lokaci kafin ya samu daidaituwa amma ya cancanci a jira shi yayin da Awoniyi ya zura ƙwallo shida daga cikin ƙwallaye takwas da ƙungiyar ta ci a watan Mayu.

Biyu sun zo ne a wasan da suka doke Southampton 4-3, ya kara cin biyu a wasa da Chelsea da ya bai wa Forest makin da take buƙata da cin Arsenal, wanda ya tabbatar da ci gaba da zaman ƙungiyar a Premier League da hakan ya kawo muhimmin farin ciki a filin wasan City Ground.

A lokacin hutu, Awoniyi ya koma Nijeriya don cika wani aiki da ke kusa da zuciyarsa, yana taimakawa wajen bunƙasa yankin da ya ba shi damar yin balaguro zuwa Turai.

Wannan matakin nasa bai-bai wa Olofinjana mamaki ba, wanda har yanzu ya ke mallakar da kuma horar da ƙungiyar Imperial FC da ke jihar Kwara.

“Taiwo ya kasance mutum ne mai kirki a koda yaushe mai matuƙar sha’awar taimakawa, idan aka yi la’akari da yadda ya tashi da kuma gwagwarmayar da ya yi,” in ji xan shekaru 43.

A watan Yuni, Awoniyi ya koma garinsu Ilorin don shirya gasa – wacce ta dace mai suna ‘Never stop Dreaming ‘.

“Wannan abu ya kasance babban buri a gare ni,” in ji Awoniyi.

“Na kasance ina fada wa kai na cewa idan wata rana zan iya (taimakawa), zan yi – kuma abin da ya sa na fara wannan abun shi ne (da fatan) in zaburar da yaran nan kuma in tabbatar mu su cewa idan har zan iya, to suma za su iya.

Sannu a hankali, wannan tsohon mai aikin ginin ya gina nasa burin na buga gasar Firimiya kuma yanzu hakan ya tabbata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *