Takardun kuɗi: CBN ya ce ba zai yi biyayya ga Kotun Ƙoli ba

*Ya ce duk mai tsohon kuɗi ya kai CBN

Daga AISHA ASAS

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce tsofaffin takardun kuɗi na N200, N500 da kuma N1000 sun daina amfani a hukumance tun daga ran 10 ga Fabrairu, 2023.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban CBN a Bauchi, Haladu Idris Andaza, yayin zantawarsa da manema labarai ranar Litinin a garin Bauchi.

Ya ce, “A tsakanin awowi 24 da suka gabata, mun samu tambayoyi da yawa daga wajen mutane game da batun tsoffin kuɗi.”

A cewarsa, “domin kawar wa jama’a shakku, muna sanar da cewa a shirye CBN yake ya ci gaba da karɓar tsoffin takardun Naira bisa wasu sharuɗɗa.

“Kwastomomi na da daman ziyartar kowane reshen CBN su miƙa tsoffin kuɗin wanda hakan ba zai yiwu ba a bankunan kasuwanci saboda tsoffin kuɗin sun daina aiki a shari’ance tun ran 10 ga wannan wata,” in ji shi.

Ya ce ana iya zuwa kowane reshe na CBN a jihohi 36 da ake da su don neman canjin tsoffin kuɗi da sabbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *