Takun saƙa tsakanin kwamitin maƙabarta da ‘yan kasuwar Kwanar tifa a jihar Kano

Daga MUKHTAR YAKUBU

A yanzu haka dai wata Sabuwar rigima ta ɓullo a tsakanin ‘yan kwamitin Maƙabartar Tudun Murtala dake jihar Kano da kuma masu gudanar da harkokin kasuwancinsu a jikin maƙabartar.

Wannan rigima kuwa ta samo asali ne a satin da ya gabata inda gobara ta tashi a cikin maƙabartar da tsakiyar rana wadda kuma har zuwa wannan lokacin ba a samu musabbabin tashinta ba.

Sai dai wasu na ɗora alhakin tashin nata a kan masu gudanar da kasuwancin su a wajen. Hakan ya sa Kwamitin Unguwar Tudun Murtala suka buƙaci masu gudanar da kasuwanci a jikin maƙabartar da lallai su tashi su bar wajen saboda tashin gobarar da Kuma wasu Abubuwan da su ‘yan kwamitin Unguwar su ke zargin masu zama a wajen suna yi wanda bai dace ba.

Amma dai tun da abin har ya zo da saka wuta a cikin ta wanda ta ƙone kaburbura masu yawa to ya zama dole su bar wajen.

Dangane wannan dambarwa da ta kunno kai, wakilinmu ya zanta da mataimakin Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar kwanar Tifar Musa Sani Babos, inda ya bayyana cewa, “Mu dai wannan kasuwa ta Kwanar Tifa da muke gudanar da kasuwanci yanzu yawan mu mun Kai sama da dubu goma, kuma dukkanmu matasa ne masu neman na kanmu.

Kuma tsawon shekaru 14 muna kasuwancin mu a wajen nan. Amma lokacin guda sai kawai muka samu labarin za a tashe mu daga wajen wai saboda wuta ta tashi a cikin maƙabartar a satin da ya gabata wanda mu kanmu ba mu san Dalilin tashinta ba.

Bobos ya ƙara da cewa, zaman su a wajen ya sa an samu tsaro ba a tare mutane a na yi musu ƙwace. Kuma ita kanta maƙabartar suna kula da ita wajen gyaran ta saboda wajen sana’arsu ne. Kuma a cewar sa.

Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta san da zaman su kuma suna biyan haraji a matsayinsu na ‘yan ƙasa masu haƙƙin yin kasuwanci a ko’ina. Inda ya yi kira ga ma’aikatar kasuwanci da Masana’antu ta jihar Kano da ta taka wa abin birki don zai iya jefa ɗimbin matasa a ƙangin rashin abin yi.

Shi ma a nasa ɓangaren, Shugaban kwamitin haɗin kan unguwar Tudun Murtala da kewaye, Alhaji Yahya Bagobiri ya bayyana wa wakilinmu cewa.

Abin da ya shafi maganar masu kasuwanci a jikin maƙabarta, asali sun nemi alfarma cewa za su zauna su rinƙa kula da maƙabarta.

Sannu a hankali kuma sai wajen ya cika da masu kasuwanci kala-kala. Wannan ya sa Abubuwa sai ƙara gaba suke yi. Sai muka ga bai kamata a ce bayin Allah suna kwance a wajen maimakon a samu nutsuwa sai hayaniya a ke samu. Sannan Kuma idan yamma ta yi, idan za ka shigo unguwar ta wajen za ka ga suna tare hanyar ma babu wajen da za a wuce.

Kuma a gaskiya idan ka duba duk maƙabartun da suke cikin kano, babu wata Makabarta da a ke kasuwanci a jikin ta sai ta Tudun Murtala, saboda Allah ya yi dai-dai?”

A don haka a cewarsa suka ga ya kamata a tashe su. Don haka muka yi ƙararsu ga hukuma.

Amma dai maganar yau za su tashi ko gobe za su tashi ya rage su da Hukumar da mu ka kai koken mu wajensu, su ne za su ɗauki matakin da ya dace wajen tashin su. Ita za ta ba su lokaci, don su ba hukuma ba ne ƙungiya ce. Hukumar da mu ka kai wa koken ita ce za ta ba su rana da lokacin da za su tashi.