Tallafa wa mazauna karkara a matsayin matakin rage talauci na Ma’aikatar Jinƙai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A kwanakin baya ne Ma’aikatar Jin Ƙai da Kula da Bala’o’i da Ci Gaban Jama’a ta Tarayya (FMHADMSD) ta fara rabon tallafin kuɗi Naira 20,000 ga matan karkara 2,900 a babban birnin tarayya da sauran sassan ƙasar nan a ƙarƙashin shirinta na ‘National Social Investment Programs’ (NSIP), domin rage talauci ga ɗaukacin al’ummar Nijeriya.

Ga mafi yawan ‘yan Nijeriya, ma’aikatar jin ƙai da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a ta tarayya (FMHADMSD), ta kasance mafi kyawun abin da ‘yan ƙasa ke alfahari da shi a sakamakon shirye-shiryenta da suka shafi mutane da yawa.

Tun farkon gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, halin da talakawa da marasa galihu ke ciki a ƙasar nan ya zama abin damuwa ga gwamnatin tarayya, wanda ya kai ga ɓullo da shirin zuba jari na ƙasa (NSIP) a shekarar 2016; a matsayin dabarun rage talauci.

Shirye-shiryen rage talauci na FMHADMSD:

Binciken da aka yi ya nuna cewa, NSIP na ɗaya daga cikin manyan tsare-tsare na kare al’umma a Afirka, inda ake ware sama da Naira biliyan 400 duk shekara don yin hidima ga rayuwar talakawa da marasa galihu a ƙasar.

Tun lokacin da aka ƙaddamar da shi a cikin 2016, NSIP ba tare da wata shakka ba ya canja rayuwar talakawa da marasa galihu a Nijeriya, tare da canja rayuwar talakawa da yawa waɗanda ke fama matsanancin talauci da waɗanda ke cikin mawuyacin hali.

Binciken da jaridar Blueprint ta yi ya ƙara nuna cewa, ya zuwa watan Yuli, 2022, sama da ‘yan Nijeriya miliyan 12 ne suka ci gajiyar ayyukan hukumar ta NSIP a cikin shekaru biyar da suka gabata, ciki har da kusan miliyan ɗaya da suka kammala karatun digiri a ƙarƙashin shirin ‘N-Power’ a ajin A, B da C a duk faɗin ƙasar, kowa ya koma gida da albashin N30,000 duk wata.

Har ila yau, kusan 300,000 da ba su kammala karatun digiri ba a halin yanzu suna samun horo da kuma ƙarfafa kayan aiki, baya ga biyan Naira 10,000 kowane wata na tsawon watanni 9.

Haka kuma, kusan gidaje miliyan 12 matalauta da marasa galihu ne aka rubuta a cikin rajistar jin daɗin jama’a ta ƙasa (NSR), wanda daga cikin gidaje miliyan 2 ne aka hako matsuguni da marasa galihu a cikin rajistar masu cin gajiyar ƙasa (NBR), waɗanda ke karɓar tsabar kuɗi Naira 5,000 duk wata.

Haka zalika nan, ɗalibai miliyan 9.8 daga Firamare 1-3 a faɗin ƙasar suna samun abinci mai gina jiki da masu dafa abinci sama da 100,000 suka shirya waɗanda dukkansu mata ne, yayin da kusan ’yan Nijeriya miliyan 3 suka ci gajiyar shirin bunƙasa kasuwanci na gwamnati (GEEP), inda ma’aikatar ta bayyana cewa, kimanin miliyan ɗaya ne za su amfana su kuma samu damar lamunin GEEP nan ba da jimawa ba.

Tallafin kuɗi Naira 20,000 ga marasa galihu:

A daidai lokacin da annobar cutar Korona ta ɓulla a shekarar 2020, FMHADMSD ta ƙaddamar da Tallafin Kuɗi ga Matan Karkara, domin ɗorewar tsarin haɗa kan al’umma na gwamnatin Shugaba Buhari.

A ƙarƙashin shirin, ana ba wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin kuɗi naira dubu 20,000 kowane lokaci don kafa ko saka hannun jari a harkokin kasuwancin da ake da su; domin fitar da iyalansu daga ƙangin talauci.

A ranar 28 ga watan Yuli, matan karkara aƙalla 2,900 a faɗin ƙananan hukumomi shida na babban birnin tarayya (FCT) sun karvi Naira 20,000 na tallafi daga Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin hukumar NSIP.

Da ta ke jawabi yayin bikin ƙaddamar da rabon tallafin ga mutane 2,900 da suka ci gajiyar tallafin a Abuja, ministar harkokin jin ƙai, kula da bala’o’i da ci gaban jama’a, Sadiya Umar Farouq, ta ce, shirin yanzu za a yi wa laƙabi da  ‘Grant for Vulnerable Groups’ (GVG), domin a ƙarfafa haɗa kai, ta ƙara da cewa, matan karkara a jihohi daban-daban na tarayya suma za su sami tallafin sau ɗaya.

Ta ƙara da cewa, “bisa la’akari da yadda masu cin gajiyar NSIP ke canja rayuwa, shugaba Buhari cikin jin daɗi ya amince da faɗaɗa shirin don taɓa rayuka da kuma fitar da ‘yan Nijeriya da dama daga ƙangin talauci.

Da amincewar shugaban ƙasa, za mu ruɓanya ayyukan yi da samar da wadata ga matasa masu tasowa a ƙasar nan, ciki har da babban birnin tarayya da ƙara yawan masu cin gajiyar Ciyarwar Makarantu, Canjin Kuɗi, da lamunin GEEP.

“Za kuma mu ƙara himma wajen ganin an ɗore da aiwatar da waɗannan shirye-shirye na tallafawa talakawa fiye da wannan Gwamnatin ta yadda Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa a kan turbar kawar da fatara da kuma cimma burinmu na ci gaban aasa da duniya nan da shekarar 2030.

“A ƙarƙashin GVG, tallafin kuɗi na Naira 20,000 ne ake raba wa mata talakawa da matasa a faɗin Jihohi 36 na tarayya da babban birnin tarayya Abuja. Burinmu a FCT shine mu raba tallafin ga sama da masu cin gajiyar 2,900 a faɗin ƙananan hukumomi 6.

“Kamar yadda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi tarayya da jama’a, kashi 70 cikin 100 na waɗanda za su ci gajiyar tallafin na mata ne yayin da sauran kashi 30 na matasa ne.”

Ministan ya ƙara da cewa, “bugu da ƙari, kusan kashi 15% na adadin waɗanda suka amfana an ware su ne musamman ga ɓangaren jama’a masu buƙatu na musamman, waɗanda suka haɗa da nakasassu (PWDs), ’yan gudun hijira (IDPs) da kuma manya a babban birnin tarayya Abuja.

Tallafin tsabar kuɗi da muke bayarwa a yau ana sa ran zai ƙara samun kuɗin shiga da kadarorin da masu cin gajiyar shirin za su amfana, musamman idan ƙalubalen tattalin arziki a matakin duniya da na gida ke shafar yanayin zamantakewar al’ummarmu.

A na ta jawabin, Shugaban gudanarwa na Canjin Kuɗi na Ƙasa, Hajiya Halima Shehu, ta kuma bayyana cewa, GVG yanzu haka ta samu cikakken iko.

“Daga ofishin karɓan kuɗi na ƙasa, mun yi cikakken tsari. Muna da sama da mutane miliyan 1.9 da suke da asusun NUBAN a bankunan kasuwanci na ƙasar nan. Wannan babban ci gaba ne saboda bayanai sun nuna cewa babu wani shiri na irin wannan da ya samu irin wannan nasarar.

“Watannin shida da suka gabata, mun dakatar da tantancewa. Yanzu duk waɗanda suka ci gajiyar mu suna da katin zare kuɗi daga bankuna daban-daban a faɗin ƙasar nan. Mun ba su horo da horarwa da yawa a fannin kuɗi don haka a yanzu za mu iya cewa an haɗa su da kuɗi domin a yanzu sun cika bankuna,” inji ta.

Manyan ’yan ƙasa ba a bar su ba so ma:
Yayin da mutane da yawa ke yin watsi da tsoffi musamman manyan ’yan ƙasa, bisa hujjar cewa ba su da wani abin da za su iya yi, Farouq ta yi imanin cewa suna da abubuwa da yawa da za su iya bayarwa, kasancewar sun shafe shekaru suna yi wa Nijeriya hidima a wurare daban-daban.

Da ya ke jawabi a ranar 28 ga watan Yuli, a yayin bikin cika shekara guda da kafa cibiyar kula da tsofaffi ta ƙasa (NSCC), Ministan ya sake jaddada buƙatar tattara bayanai kan tsofaffin mutanen da suka tsufa domin a samar musu da isassun abin da ya dace da kuma rage masu rauni.

“Yayin da yawan tsofaffi ke ci gaba da ƙaruwa a Nijeriya, ina roƙon ku da ku faɗaɗa ayyukanku ta hanyar shigar da gwamnatocin jihohi don ƙara haɗin gwiwa. Akwai buƙatar faɗaɗawa da ingantattun bayanai da nazarin yawan mutanen da suka tsufa don taimakawa masu tsara manufofi don ayyana, tsara manufofi da shirye-shirye, wayar da kan jama’a da goyan bayan canje-canjen manufofin da ake buƙata.

“Muna farin cikin murnar cika shekara ta farko da ƙaddamar da cibiyar ’yan ƙasa ta ƙasa. Ba za mu iya ci gaba da yin watsi da tsofaffin mu ba bisa la’akari da gogewarsu, iliminsu da ƙwarewarsu a cikin al’umma. An daɗe ana watsi da tsoffi a cikin al’ummi kuma lokacin ɗaukar matakin gaggawa da shiga tsakani ya yi yanzu.”

Da ta ke miqa godiyarta, ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin CVG a FCT, Elizabeth Lalu, ta yabawa Farouq da ɗimbin shirye-shiryen da ta ke yi wa talakawa, inda ta ce, tallafin N20,000 zai taimaka ma ta wajen farfaɗo da ƙananan sana’o’inta.

Har ila yau, Grace Sunday, mai sana’ar kula da gashi, ta ce, tallafin zai ba ta damar sayen wasu abubuwa domin buƙatar ta kan yi mata wahala ne sakamakon ƙarancin kuɗaɗe.

“Ɗaya daga cikin abokaina ya ce, in aika sunana ta wata ƙungiya mai zaman kanta, na aikata. Na sami saƙon da zan zo don tallafi a yau. Ina sayar da turare mai. N20,000 zai kawo gyara fuska ga kasuwancina. Turaren suna da ɗan tsada, amma zan iya samun ƙarin da wannan tallafin. Zan tuntuvi ƙarin abokan cinikina.

“Kuɗin za su yi nisa kamar yadda zan saya fiye da adadin da na saba saya. Wani lokaci, buaatun yana da yawa, amma yawanci ba ni da kuzi don saduwa. Don haka da wannan kuɗin maimakon in sayi fakiti 5 na turaren mai, yanzu zan sayi guda 10 ko sama da haka. Don haka, ba zan iya samun isassun kalmomi da zan gode wa ministar ba, amma Allah ya sani ina godiya da wannan shiga tsakani,” inji ta.

A nata ɓangaren, Misis Grace Agu, ta gode wa shugaba Buhari bisa wannan karamcin da ya yi mata, inda ta ce kuɗaɗen za su tallafa wa ƙananan sana’o’in da ta ke yi da kuma fitar da ita daga ƙangin talauci.