Tallafawar tsofaffin ɗalibai a makarantun da suka gama na da mutuƙar muhimmanci – Hafsat Madigawa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yi kira ga tsofaffin ɗalibai akan su riƙa bada gudunmuwa domin cigaban makarantun da suka samu ilimi a ciki ta yadda za su kyautata su domin amfanin ‘yan baya, su samu ilimi mai inganci  da shi ne ƙashin bayan duk wani cigaba na al’umma.

Hajiya Hafsat Hamisu Ali Madigawa, ɗaya daga cikin tsofaffin ɗalibai na makarantar Fukara’u da Assahaba ce ta bayyana haka da take zantawa da ‘yan jarida. 

Ta ce taron tsofaffin ɗalibai abin farin ciki ne ga duk wanda ya saka ƙafafuwansa a makarantar su mai albarka musamman tun da suka gama daga 1982 zuwa yanzu ba a taɓa taro makamancin wannan ba suna farin ciki mara misaltuwa da godewa Allah.

Ta ƙara da cewa a matsayinta ta tsohuwar ɗaliba tana cike da ƙudiri a ranta koyaushe na tallafawa ilimi saboda ko yaya kana so kaga wurin da ya amfanar da kai ka samu ilimi da ya zamar da kai yadda kake a yau kai ma kana so ka ga wani cigaba a tare da shi don haka ba sau ɗaya ba ba biyu ba suna tattaunawa  akan neman mafita da yanda zasu taimakawa cigaban makaranta.

Ta  yi nuni da cewa ƙofar su a buɗe take  a duk lokacin da buƙata irin haka ta taso suna buƙatar a riƙa tuntuɓar su in Allah ya yarda za su kawo tallafinsu ga cigaban makarantar domin samun cigaba kuma shi maganar tallafawa ba sai kana da shi ba in dai kana da hamasa na son kaga kayi abu komai ƙanƙantar sa ko ya ya yake sai kaga Allah ya yi maka a cikin ƙudirar sa da buwayarsa don haka yan’uwanta tsaffin ɗalibai maza da mata a duk inda suke su dage su haɗa kai su taimaka dan kawowa makarantun cigaba suyi fice yanda za suyi gogayya da dukkanin sauran makarantu.

Hajiya Hafsat ta ce za su yi duk mai yiwuwa za su tura a duk inda suke son saƙo ya je in Allah ya yarda, za su yi wannan ƙoƙarin kuma su kawo cigaba a Gwamnatance da ta ɓangaren harkar kasuwanci da kuma ƙarƙashin ƙungiyar su ta tsofaffin ɗalibai domin su sami nasarar kai makarantun matakin da ake buƙata.

Sannan ta jaddada kiran ta ga sauran al’umma su farka idan aka yi duba da yadda al’amura ke tafiya na matsalolin ilimi jihohin mu na na Arewa na buƙatar tallafi saboda akwai gazawa a wasu ɓangarorin da ya kamata a ce an haɗa kai domin a gudu tare a tsira tare.

Hajiya Hafsat Hamisu Ali Madigawa ta ce gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf kullum bada tallafi take akan abinda ya shafi cigaban ilimi koyaushe su burinsa su ga ilimin nan yanda ake tunanin kudancin ƙasar nan sun yi zarra su tarrad dasu suma wuce su, wannan kuwa koyi ne da suke da jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da ya ɗora su akan kishin bunƙasa cigaban ilimi domin jihar Kano ta yi fice.