Tallafin mai: Tsakanin gaskiya da ƙarya

Daga FATUHU MUSTAFA

Na lura mutane har yau ba su fahimci gaskiyar abinda ke faruwa game da tallafin mai da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ke baiwa talakawa ba. Ba kuma su fahimci illar da tallafin yake wa al’amuransu na yau da kullum ba.

Kamar dai yadda Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya tava faɗa ne, “Mutane sun fi damuwa da illar cire tallafin man fetur, fiye da illar barin sa”.

In har tallafin mai yana da wani alfanu ga talakan Nijeriya, to bai wuce na sauƙaƙa tsadar man ba, wanda in an masa kallon na tsanaki, tuni wannan dalili ya kai, saboda matsalar almundahana da rashin gaskiya da ya yi katutu a zukatan su attajiran da ke amfana da kasuwancin man fetur din.

An kiyasta cewa, a shekarar 2022 kawai, gwamnatin tarayya ta kashe sama da Dalar Amurka biliyan Goma domin biyan kuɗin tallafi ga farashin man fetur ɗin.

Mutum ya yi la’akari da cewa, matatar mai ta Dangote wacce ta fi kowacce girma a duniya, an gina ta ne a kan kuɗi Dala biliyan 19, ka ga kenan muna kashe kudin da za mu gina matatar mai guda a shekara 2 kacal! Ka yi tunanin in amfani akai da kuɗin aka gina matatar mai a sabon gurbin da aka haƙo mai a Gombe.

Abin tambaya, su wa ake bai wa kuɗin? Me ya sa duk da waɗannan maƙudan kuɗaɗe amma man fetur ke tsada a Nijeriya? Anya kuwa ba kura da shan bugu, gardi da karve kuɗi ake ba?

Bari mu ga yadda abin yake a sauƙaƙe. Da farko dai in ka sayo mai daga waje, za ka kawo shaida ne ga hukumar kula da albarkatun mai ta qasa wato DPR da ke Ikko (kar a manta, kamfanin NNPCL, aikinsa bai shafi nan ba, aikin sa shi ne hakowa da sayar da ɗanyen mai ba tatacce ba).

Ita hukumar ita za ta saye man, sannan ta ba ka shaidar da za a biya ka kuɗinka. Wannan hukuma ta kan sayi man ne ta ɗora maka riba. Misali ka sayo shi a kan $2 ita kuma sai ta saye shi a kan $3, sai ta biya ka, wanda ya haɗa har da kuɗin jigila da sauransu.

Sai ita kuma ta karyar da shi, ta sayar da shi a kan farashin da dan ƙasa zai iya saya. A ɗauka a kan $1.5. In ka lura wannan sauqi ne aka yi wa ɗan ƙasa. To amma mai karatu zai tambayi kansa, shin a ina matsalar take, me ya sa man duk da haka yake tsada?

Abinda ke faruwa shi ne, attajirin da ya sayo man nan a $2 ƙila ya sayo lita miliyan ɗaya a kan $2 miliyan, ya samu ribar $1 miliyan kenan. To shi ne dai zai zagaya ya koma wurin kamfanin, ya sayi kowacce lita a $1.5, amma fa ba a nan ta tsaya ba, sai kuma ya ɗauki takardar sai ya kai wata hukuma da ake kira Petroleum Equalisation Fund, wato hukumar daidaita kuɗin man fetur, wacce ita kuma ke da alhakin tabbatar da cewa an sayar da mai a kan farashin baiɗaya a ƙasa.

Aikinta shi ne ta biya ka kuɗin sufurin mai da za ka ɗauko daga Legas ko Fatakwal zuwa wasu sassa na ƙasar nan. Saboda in ka kawo ka sayar da shi, kamar yadda za ka sayar a can inda ka ɗauko man. To a maimakon shi wannan attajirin ya kawo man ya sayar da shi a kan wannan kuɗi da hukuma ta ba shi man a kai, tunda ya gama cin riba tun kafin man sa ya zo kasuwa, sai ya ɗau ɗaya daga cikin matakai biyu, walau dai ya tsawwala farashin a kan talakawa, ko kuma ya karkatar da man zuwa wasu ƙasashe da ke makwabtaka da Nijeriya inda man ke da tsada fiye da ƙasar nan.

In an kula, gabaɗaya waɗannan kuɗaɗe sama da dala 4 a kan kowacce lita, daga lalitar gwamnati yake fitowa domin a sawwaƙa wa talakan Nijeriya. Waɗannan kuɗaɗe dai, su ne kuɗaɗen da za a yi muku tituna, makarantu, asibitoci, a saya wa jami’an tsaro kayan aiki, amma ga su sun tafi a biyan wasu mutane ‘yan ƙalilan, su kuma tsabar handama da babakere da rashin godiyar Allah, maimakon su riqe amana, su sayar wa talaka mai a farashi mai rahusa, sai su karkatar da man zuwa wata nahiyar, ko su tsula wa talaka kuɗi.

Kowa ya san Nijeriya ce ta fi kowacce ƙasa a Afirka arahar man fetur, wannan ya sanya attajiran man fetur ɗin, da suke sayan sa a farashi mai rahusa, suke amfani da wannan dama, sai su ƙetare da man da suka saya a hannun gwamnati zuwa ƙasashen Kamaru ko Nijar ko Chadi, inda sukan sayar a farashi mai tsada. Wannan dalili ya sanya, kashi 70% na yawan man da Nijeriya ke saya, ba ya amfanar talakan Nijeriya. Wasu ‘yan ƙalilan ne kawai suke cin karensu babu babbaka, suke sharholiya da damar.

Wannan ya sanya, kashi 40% na kasafin kuɗinmu na kowacce shekara, yana tafiya ne wurin biyan wasu ‘yan tsirarun attajirai, waɗanda ke haɗa kai da wasu ƙungiyoyin ma’aikata suna yaɗa farfagandar za a sanya talaka cikin halin ni ‘ya su. Wanda a zahirin gaskiya, cire tallafi ba talaka ba ne zai shiga halin ni ‘ya su, su ne za su rasa hanyar da suke wawure kuɗaɗen mutane.

Kai sau da dama ma, wasu gwamnatocin, ‘ya’yansu da aboka su da matansu sukan bai wa wannan lasisi na shigo da mai. Da haka suke yashe mana ‘yan kuɗaɗen da za a yi mana ayyukan raya ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *