Tallafin man fetur na kowane ɗan ƙasa ne, cewar Gwamna Sule

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule ya gargaɗi waɗanda ke rabon kayayyakin tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar ta Nasarawa su tabbatar suna nuna gaskiya da riƙon amana su kuma guji son kai da sauran su ayayin da suke raba tallafin ga al’ummar jihar baki daya ko su fuskanci fushin gwamnatinsa.

Gwamnan ya yi gargaɗin ne a lokacin da ake bikin ƙaddamar da rabon kayayyakin abinci na tallafin man a ƙaramar hukumar Karu a jihar ranar Laraba na mako da ake ciki 6 ga watan Satumbar shekarar 2023.

Ya ce kiran ya zame wajibi idan aka yi la’akari da yadda sau da yawa idan irin wannan tallafi ya samu za a ga wasu musamman ‘yan siyasa na nuna son kai suna kuma sa siyasa a lamarin maimakon kowa ya samu.

Ya ce akan haka nema ya sa ya yanke shawarar ya riqa kasancewa da kansa a wajen rabon kayayyakin don tabbatar cewa waɗanda suka cancanci samun tallafin ya iso gunsu.

Gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar cewa gwamnatin tarayya ta ware kimanin kuɗi Naira biliyan 5 ne wa jihar don tallafa wa talakoki wajen rage musu wahalhalu da cire tallafin man fetir ɗin ya jawo inda ya ce kawo yanzu gwamnatin tarayyar ta bai wa gwamnatinsa Naira biliyan 2 ne inda ta ce nan bada daɗewa ba za ta ba ta sauran biliyan 3 da ya rage don cigaba da rabon.

Gwamnan ya kuma yi ƙarin haske dangane da tsarin rabon tallafin inda ya bayyana cewa an tsara kowane ma’aikacin gwamnatin jihar zai riƙa karvan Naira dubu 10 a kowane wata har na watanni 6 nan gaba yayin da su kuma ma’aikatan qananan hukumomin jihar da waxanda ke karvan fansho za a riƙa basu Naira dubu 5 a kowane ƙarshen wata.

Su kuma gajiyayyu da talakawa za a ba su buhunan shinkafa da sabar kuɗi Naira dubu 5 nan take a wajen rabon da sauransu.

Gwamna Abdullahi Sule ya kuma yi amfani da damar inda ya jinjina wa gwamnatin tarayya ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da hangen nesa da ta yi na tallafa wa al’ummar ƙasa baki ɗaya da tallafin a wannan mawuyacin hali da cire tallafin ya jawo inda ya buqaci al’ummar ƙaramar hukumar ta Karu da sauran waɗanda suka amfana da tallafin daga wasu ƙananan hukumomin jihar kawo yanzu su tabbatar sun yi kyakkyawar amfani da tallafin.

Tun farko a jawabin Shugaban karamar hukumar Karu a jihar honorabu James Thomas ya sanar wa gwamnan jihar da sauran mahallata taron yanayin tsarin rabon kayayyakin ne inda ya kuma tabbatar masa cewa mahukuntan karamar hukumar za su tabbatar sun sauki nauyi dake wuyar su ta rabon kayayyakin yadda yakamata sannan su tabbatar wadanda aka zakulo za su fara amfana daga yankunan karamar hukumar ne za a tabbatar sun fara amfana inda ya buƙaci hadin kan jami’n tsaro da al’ummar karamar hukumar ta Karu baki ɗaya don tabbatar da nasarar rabon akarshe.

Wakilin mu dai ya gano tuni dai aka fara rabon kayayyakin tallafin da suka hada da buhunan shinkafa da sabar kudi da dai sauran su wa mazauna karamar hukumar ta Karu jim kaɗan bayan an ƙaddamar da fara rabon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *