Tallafin naira biliyan 600 ga manoma

Labarin da aka bayar cewa Gwamnatin Tarayya na shirin bada tallafin sama da naira biliyan 600 don agaza wa manoma abin farin ciki ne. Ba shakka, abin da ya dace ne idan har ana so a faɗaɗa hanyoyin inganta tattalin arzikin ƙasar nan, wanda ya shafe sama da shekara hamsin ya na dogaro da man fetur wajen samun kuɗaɗen shiga.

Ministan Aikin Gona Da Raya Yankunan Karkara, Alhaji Sabo Nanono, shi ne ya bayyana labarin a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na ma’aikatar sa, Mista Theodore Ogaziechi, ya rattaba wa hannu kwanan nan a Abuja.

A sanarwar, an ce ministan ya faɗi haka ne lokacin da ya kai ziyara a kamfanin yin takin zamani na Ɗangote da wasu kamfanonin yin taki da ke Jihar Legas.
Nanono ya ce za a bada tallafin ne ga qananan manoma marasa ƙarfi a duk faɗin ƙasar nan don ganin sun samar da abincin da za a ci, kuma za a za a fara ne da manoma miliyan biyu da dubu ɗari huɗu. Amma fa ya ce don kada wasu su vata kyakkyawar manufar gwamnati ta hanyar shigo da hanyoyin cuta, ba tsabar kuɗin za a bayar ba kamar yadda ake yi a baya, a’a, kayan aiki za a raba. Ministan ya ƙara da cewa rufe dukkan kan iyakokin ƙasar nan da aka yi, wanda annobar korona ta tilasta yin hakan, ya nuna cewa Nijeriya za ta iya ciyar da kan ta cikin sauƙi ba tare da wata matsala ba.

Ministan, wanda ya soma da kai ziyarar ban-girma ga Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi alƙawarin zai taimaka wa manoman da ke yankunan karkara a jihar da ƙananan hanyoyin mota da wuta mai aiki da hasken rana da wuraren samun ruwan sha don su ƙara yawan aikin su.

Bugu da ƙari, Nanono ya yi alƙawarin zai haɗa gwiwa da gwamnatin Jihar Legas domin inganta harkar kamun kifi ta hanyar haɓaka wuraren da ke da ruwa a jihar don rage shigo da kifi daga ƙasar waje.

A nasa jawabin, Sanwo-Olu ya yi alƙawarin zai haɗa hannu da Gwamnatin Tarayya ba ma a sashen kamun kifi kaɗai ba har ma da ɓangaren aikin gona na zamani. Gwamnan ya ce za a aiwatar da hakan ne bayan an gama gina masana’antar casar shinkafa da ta fi kowace girma a Nijeriya inda za a riƙa samar da shinkafa kimanin tan miliyan 30.  Ya ce hakan zai taimaka wa Nijeriya wajen maida hankali ga fitar da shinkafa ƙasar waje tare da rage farashin ta a kasuwa.

Gwamnan ya ce Jihar Legas ta na da manya-manyan kasuwannin sayar da amfanin gona da kuma kamfanin da ya fi kowane girma wajen taimakon aikin gona, wato kamfanin sarrafa takin zamani na Ɗangote wanda aka kafa a cikin jihar.

A nasu ɓangaren, kamfanin Ɗangote Group da sauran kamfanonin yin takin zamani da su ka haɗa da Premium Agro Limited, Elephant Group da Kewalram Group, sun yi kukan cewa su na fuskantar matsalar kayan da ake buƙata kafin a yi takin zamani, su ka  ce musamman ma dai sinadarin nan na ‘ammonium phosphate’, ya fi ba su wahala.

Duk da haka, shi kamfanin Ɗangote Group, ya bada tabbacin cewa zai duba yiwuwar samun wasu hanyoyin na cikin ƙasa domin samun wannan sinadarin wanda ake fatan zai taimaka wajen rage matsalar rashin isasshen kayan aikin yin takin zamani a ƙasar nan.

Masana ilimin tattalin arziki, irin su Farfesa Samuel Onasanya na Jami’ar Ilorin, sun kawo shawarar cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta bari naira ta riƙa yawo a ko’ina ba tare da takurawa ba, sannan a zamanantar da aikin gona, kuma a gyara harkar man fetur a matsayin hanyoyin da za a bi a fitar da ƙasar nan daga halin karayar tattalin arziki da ake fuskanta a yau. Onasanya, wanda farfesa ne na kimiyyar harkar ilimi, ya yi kiran ne a lokacin da ya ke gabatar da wata maƙala a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Osiele, Abeokuta.

A laccar tasa, malamin ya yi nuni da buƙatar da ke akwai ta Nijeriya ta faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shigar ta ta hanyar zuba jari a inda ya dace. Ya ce idan aka ƙara yawan abinci har ana fitar da shi ƙasar waje, to karayar tattalin arziki za ta ragu har Nijeriya ta hau matsayin ta da ake ta tutiya da shi na ‘uwar Afrika’.

A cewar Farfesa Onasanya, “A shekarun 1960, aikin gona ne ke rije da tattalin arzikin ƙasar nan wajen samar da kuɗaɗen shiga da kuɗaɗen musanya da samar da aikin yi”. Daga nan ya bada shawarar cewa “a sanya aikin gona ya zama mai kawo riba ga matasa ta hanyar samar da kayan aiki na zamani da rancen jari da zai taimaka a yi aikin gonar a zamanance.”

Malamin ya yi nuni da cewa, “Nijeriya na da buqatar ta faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi daga kayan da ta ke sayarwa a ƙasar waje da inganta masana’antun ta ta hanyar zuba jarin da ya dace, idan ba haka ba kuwa to za a wayi gari a ga cewar arzikin ta bai iya riƙe yawan jama’ar ta.”

Onasanya ya ƙara da cewa tsarin tattalin arziki na duniya ya jima da karyewa kuma ba a fara samun sauƙi ba har sai da aka ɗauki lokaci mai tsawo, musamman daga 2016. Ya ƙara da cewa akwai alamun gwamnati ta ɗauki wasu matakai na rage hauhawar farashi ta hanyar cire wasu muradai na masu shigo da wasu kayayyakin sayarwa.

Malamin ya ba gwamnati shawarar ta rage kuɗin haraji da ta ɗora wa jama’a da ƙananan sana’o’i da kamfanoni da kashi 10 cikin ɗari saboda a bada ƙwarin gwiwa ga masu son zuba jari a waɗannan sassan na tsarin tattalin arziki. Ra’ayin sa shi ne masu zuba jari za su ji daɗi idan an rage masu haraji.
Saboda haka, bayan mun dubi muhimmancin samar da abinci ga cigaban tsarin tattalin arziki da na siyasar ƙasar nan ne mu ke ba Gwamnatin Tarayya shawara cewa kuɗi naira biliyan 600 da aka ce za a ba ƙananan manoma sun dace.

To amma fa ya kamata gwamnati ta gaggauta aiwatar da wannan shirin tare da tabbatar da cewa an aiwatar da shi a bayyane ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba.