Tambuwal ya sha da ƙyar a takarar Sanatan Sakkwato ta Kudu

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi nasarar lashe kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu da ya nema.

Baturen zaɓen yankin, Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo, shi ne ya sanar da nasarar Tambuwal inda ya ce ya samu ƙuri’u 100,860 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin karawarsa na APC, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba wanda ya tsira da ƙuri’u 97,884.

Nasarar Tambuwal ɗin dai na zuwa ne bayan da zaɓen kujerar ya kasance wanda bai kammalu ba a zaɓen yayin zaɓen ‘yan Majalisar Tarayya da aka gudanar ran 18 ga watan Maris ɗin da ya gabata.

A baya, Aminu Waziri Tambuwal ya kasance a zauren majalissar wakilai har sau uku wanda har ya zama Kakakin Majalisar a wancan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *