Tambuwal zai gina sakandare na zamani guda 40 a Sakkwato

Daga AISHA ASAS

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal, ya bayyana aniyarsa ta gina Makarantun Sakandare irin na zamani guda arba’in a sassan jiharsa.

A wata sanarwa da ya fitar, Tambuwal ya nuna ilimi shi ne ƙashin bayan cigaba a cikin kowace al’umma.

Ya ce ayyukan da gwamnatinsa ta sa gaba wajen inganta fannin ilimin jihar, da suka haɗa da yi wa makarantun firamare 1,500 da ƙananan sakandare 180 kwaskwarima, wata alama ce da ke nuni da yadda gwamnatinsa ta ɗauki fannin ilimin jihar da muhimmancin gaske.

Kazalika, ya ce gwamnatinsa ta damu da batun yaran da ba su tafiya makaranta a jihar, don haka ya jaddada cewa gwamnatinsa na da ƙudirin gina ƙarin makarantun firamare da na sakandare domin magance matsalar.

Tare da cewa, gwamnatin jihar da ma ta tarayya sun dukufa ɗaukar matakan magance Almajirci a jihar lamarin da a cewar gwmnan ya yi sanadiyar hana yara da daman gaskiya tafiya makaranta boko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *