Tantance Ma’aikata: Gwamnatin Zamfara ta bankaɗo ma’aikatan bogi 2,363 da samun rarar sama da N200m

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnatin Zamfara ta ce ta gano ma’aikatan bogi kimanin mutum 2,363, biyo bayan kammala aikin tantance ma’aikatan gwamnati a jihar.

Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance Ma’aikatan ne a ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikatan jihar a watan Agustan 2024 tare da umarnin gudanar da aikin tantance ma’aikata.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce aikin tantancewar ya bankaɗo ƙananan yara 220 da ke karbar albashi duk wata a matsayin ma’aikatan gwamnati.

Sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan ƙoƙarin gwamnatin jihar ne na aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000.

“Domin inganta ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya kafa wani babban kwamiti da aka ɗora wa alhakin tantance albashin gwamnatin jihar.

“Kwamitin tantancewa ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikata na jihar Zamfara ya haɗa da kwamishinan kudi, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta jihar Zamfara, babban akanta janar, babban mai binciken kuɗi, babban jami’in ƙididdiga a matsayin mambobi, da kuma sakataren zartarwa na ZITDA a matsayin sakatare”, inji Kakakin.

Ya ce “Haƙƙin farko na kwamitin ya haɗa da tabbatarwa da haɗa tsarin ƙima da tsarin biyan albashi da ƙirƙirar fayilolin ma’aikata na lantarki.”

Ya ƙara da cewa, “Rahoton ƙarshe da kwamitin ya miƙa wa Gwamna Dauda Lawal ya nuna cewa ma’aikata 27,109 na dindindin ne aka sallame su, yayin da ma’aikatan da ake da shakku akansu sun haɗa da ma’aikatan bogi 2,363, ma’aikatan gwamnati 1082 da za su yi ritaya, 395 ma’aikatan kwangila, 261 ba na takardar sheda ba, 213 na hutun karatu, ƙananan yara 220 kuma na biyu a aikin yi”, inji shi.

Kazalika, ya ce a yayin tantancewar an fallasa ma’aikatan bogi 2,363. “ana biyan su jimillar Naira miliyan 193,642,097.19 a kowane wata.”

“Ma’aikata 1,082 da za su yi ritaya kuma suna karɓar jimillar kuɗi N80,542,298.26 a duk wata. A lokaci guda kuma, ma’aikata biyar da aka gano suna aikin boko, ana biyansu duk wata N354,927.60.”

Kwamitin ya bada shawarar dakatar da ma’aikata 207 da ba a wanke su ba, waɗanda ana biyansu jimillar albashin N16,370,645.90 duk wata.