Taraba: Shugaban ƙaramar hukuma ya tsallake rijiya da baya

Daga UMAR M. GOMBE

‘Yan bindiga sun kai wa Shugaban Karamar Hukumar Takum, Shiba Tikari, a jihar Taraba hari inda ya samu ya tsallake rijiya da baya.

Harin wanda ya auku Asabar da ta gabata a ƙauyen Dogo-Gawa, ya yi sanadiyar rasa ran ɗan sandan da ke bai wa shugaban tsaro sakamakon wuta da tsegerun suka buɗe wa motocinsu.

Manhaja ta gano cewa ɗan sandan da ya rasa ransa a harin na ɗaya daga cikin ‘yan sandan kwantar da tarzoma su 67 da aka girke a yankin ƙaramar hukumar.

A wata sabuwa, bayanai sun nuna ‘yan sandan Ƙaramar Hukumar Wukari a jihar, sun yi nasarar daƙile wani yinƙurin sace mutane da aka yi a ƙauyen Choku inda aka yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaton da ɓarayin.

Binciken Manhaja ya gano cewa a ‘yan kwanankin baya-bayan nan, yankin Takum da Wukari dukkansu a yankin kudancin jihar Taraba, na fama da matsin lambar ‘yan ta’adda.

A lokacin da yake tabbatar wa manema labarai da faruwar harin, Tikari ya ce tawagar ‘yan bindigar sun buɗe wa motocinsu wuta ne a kan hanyarsu ta zuwa Takum.

Da wannan dalili ne shugaban ƙaramar hukumar ya yi kira da a tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin don ci gaba da bai wa jama’a kariya.