Tarbiyyar yara a ƙasar Hausa: Da sauran rina a kaba!

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Da fatan na same ku lafiya, Allah ya ba mu wuce wannan sanyi lafiya. Ga mu yau ma kamar kullum cikin filinmu mai albarka, filin koya tarbiyya.

Yau za mu tavo yadda muka yi sakaci da rayuwa, muka sa son zuciya da bushewarta, har shaiɗan ya yi galaba cikin rayuwarmu. Mutane mun zamo marasa imani, da rashin tsoron Allah.

Da yawa mun fifita kuɗi a kan neman Lahira.Tarbiya ta daɗa nisa da mu, yara ƙanana mun koya musu son abun duniya da neman kuɗi ta kowacce hanya. Yara sun ƙeƙashe zuciya da muguwar rayuwar da suka ga muna yi.

Babu wanda bai kaɗu ba a kan irin rayuwar da yanzu muke gudanarwa ba, ta sace yara ko manya a yi garkuwa da su, a nemi kuɗi ba na wasa ba, don ka fanshi wani naka.

Innalillahi wa’inna ilaihi raji’una!  Mun manta yanzu da zaman lafiya, da muna tararrabin bin hanyoyi kar ka tafi a ɗauke ka. Yanzu ta kai har cikin makarantu, inda kake da yakinin yaronka ya tsira. To yanzu nan ma ta zama shalkwata ta tararrabi.

Makarantun kwana ma inda muke zaton akwai tarbiyya da sa ido a kan yaranmu, nan ma ba ta sake zani ba. Yaranmu ba abin da suke koyowa sai ta’addanci.

Yaro yana ɗauke da makami ba mu sani ba zai iya kasa mugun abu ga ɗalibi ɗanuwansa, to wai ina mafita ne?
Kallace-kallace ke jawowa, yadda a film yara za su ga an yi garkuwa da mutum an kawo kuɗi mai yawa an ba da, an saki mutum. Ko an hana, an kashe. Sai suke ganin duk wannan ba wani abu ba ne daga lokacin da suka ga haka, sai su daɗa kangarewa, ko kuma a cikin unguwanni suke gani?
Faɗace-faɗace da suke kalla ne ko kuma meye yake jawowa ne?

Faɗar wasu abubuwa a gabansu ne yake jawo hakan ko kuwa meye? Waɗannan abubuwa abun dubawa ne. Ya kamata iyaye da gwamnati mu tashi a tsaye mu gano matsalolin da yaranmu suke son tsunduma kansu a ciki. Kuma ɗaukar mataki fa ya zama dole ga masu irin waɗannan abubuwa, saboda a daƙile wannan muguwar rayuwa da yaranmu suka ɗauko.

Babban mutum zai haike wa yarinya ƙarama ya vata mata rayuwa, babu tausayi babu kunya. Ko kuma uba ya haike wa ɗiyar cikinsa ba tare da ya yi tunanin rayuwarta ba, ko ta iyalinsa ba. Uba fa da aka sani da nema wa iyalinsa tsari, yau uba ke sahun farko wajen lalata wa ɗiyar cikinsa rayuwa.

Kenan yara mata ba su da wata rayuwa a gaba, sai dai a yi musu fyaɗe, a bar su cikin uƙubar rayuwa.
Gwamnati za ta kama masu laifi kuma ba tare data hukunta su ba, kawai sai a ga mutum ya yi watanni ya fito ya cigaba da rayuwarsa kamar ma bai yi komai ba.

Uwa tana cikin firgici kullum na tsaron ‘yarta kar ta faɗa hannun ɓata gari. Namiji kana fargaban haɗuwar sa da mugayen abokai. Kullum iyaye mata sun fi kowa shiga taskun rayuwa, ta yaya za su tsare yaransu daga wannan azzalumar rayuwa da muka tsinci kanmu?

Makarantu da muka san gidan tarbiyya ne shi ma yanzu ya fara zama abin tsoro. Domin kullum sai dai a ji an wa yarinya fyaɗe, ko kuma Malama ko Malami ya kashe ɗalibi da duka, ko ɗalibi ya kashe ɗalibi ɗanuwansa. Ya Ilahil alamina, yaya ake so ne a yi rayuwa?

Yana da kyau fa iyaye su sake sabon salon ba wa yaran su tarbiyya. Uwa ta daina biye wa ɗanta ko ‘yarta abinda suke so, su nuna musu rayuwa mai ɗorewa. Ba su wayoyi ma yana daga rusa wa yara rayuwa wallahi. Yaro da bai fi shekara 12 ko 14, ba an bashi waya babba. Don Allah ta yaya za a samu tarbiyya a nan?

Misali, jiya juma’a na fita kasuwa, ina cikin ɗan sahu idona ya hango yaran mata ɗalibai duk ba su gaza 13 ba kowacce da waya danƙareriya a hannun ta. Ta kusa da ni ta sunkuyar da kanta ƙasa tana ta kallace-kallace. Takaici ya ishe ni don wallahi na tabbata ba abun alheri take kalla ba. Kanta na ƙasa tana murmushi, ni ba abin na yi mata magana ba, a wacce hujjar?  Har na je na dawo, hoton abin ya qi gogewa a raina.

Ta yaya za mu ce ba mu muka ɓata wa yaranmu tarbiyya ba? ta yaya za mu kalli kanmu wataran a matsayin iyaye nagari?

Uba ko uwa za ta yi wa ɗanta bazde, wai ta rasa me za ta masa kyauta da shi sai waya. Ku zaga ku ga yadda yara matasa ke juya wayoyi manya a hannunsu, ku duba ku ga me suke shukawa da waɗannan wayoyi da kuka ba su. Sai kin yi karo da ɗanki ko ‘yarki a Fesbuk, ko Wasaf suna danne-danne sannan ne za ki san ba ƙaramin kuskure kika yi ba.

Na fi ba wa iyaye maza laifi. Sun fi kowa sakaci a kan gina gidajensu a tarbiyya. Kacokan sun damƙa komai a hannun mata, a matsayin ku ba mazauna ba ne.  To an ji, zaman na mata ne. Amma akwai lokacin da ya kamata ka san me iyalinka suke ciki ko?

Sai abu ya kwave ki ji uba yana kumburi yana matar ta cuce shi, ta ɓata masa suna da tarbiyyar gida. A ina da aka ce uwa ce kaɗai za ta sarrafa gida ba taimako na jigon gidan namiji. Ai hannu ɗaya ba zai taɓa ɗaukar ɗaki ba, dole sai da majingini. Taruwa za ku yi, ku tsara wa kanku yadda za ku tafi da gidanku.

Ita tarbiyya fa aba ce mai wuya kuma mai daɗi. Dole sai an mata taka tsan-tsan sannan za a ga ribarta. Duk yadda ka ɗauki rayuwa fa haka za ta ɗauke ka. Kawai mu iyaye mu dage da nuna wa yara mahimmancin abubuwa da yawa na rayuwa wanda suke masu kyau da zubar da marasa kyau, sai da lallami da nusarwa yaran yanzu za su biyu, ba duka ko zagi ne zai lafar da su ba.  Tunda Allah ya kawo mu wani zamani na iyaye ne za su bi yaran su ba wai yaran ne za su bi iyaye ba.

Su kuma yara su ji tsoron Allah su sa haƙuri da bin abinda iyaye suka ce ko bai musu daɗi ba. Don Allah iyaye mu daɗa jan yaranmu a jiki, muna koya musu abubuwa na gari, masu kyau da za su tashi da shi. A tabbatar sun mai da kansu a kan makarantar boko da islamiyya fiye da wasanni. Kar kuma a takura su da karatu babu nishaɗi.

A ware musu lokacin wasa, yadda ba zai yi tasiri ba fiye da karatu. A tabbatar sallah a kan lokaci da tsoratar da su abinda Allah Ya tanada ga wanda ya kauce mata, zai taimaka masu su sanya taka-tsan-tsan cikin al’amuransu.

Iyaye su zamo masu faɗar alheri a kan yaransu fiye da kassara su da baki. Ya kasance iyaye na lura da dukkan motsin yaransu, banda fita barkatai. A tabbatar an san inda suke zuwa, ko da wa suke fitar. Cikin gidanki ma ba ki sani ba sai yaro ya aikata laifi kina zaune hangam. Rayuwa ce ta yanzu ta zama zuma sai wanda ke da juriyya zai sha.

Ba a hana yara kallo ba. A’a a dai kula da irin fina-finan da za su kalla. A janye musu duk wanda aka san za su ɓata musu tunaninsu.

Kada a rinƙa barin yara da makamai a hannunsu don Allah. Da zarar yara sun ɗau makami, a yi ƙoƙarin nuna masu illar su ta yadda ko a gun wani suka gani, za su ƙyamaci abun.

Mu fa tashi a tsaye mu sama wa kanmu mafita don yanzu idan ka sa ƙiwa a ranka, to za ka ga babban aiki. Rayuwar yanzu abar tsoro ce, idan ba ka iya ba, Duniya za ta koya maka darasin da baka taɓa shiga ajinsa ba. Allah Ya raba mu da aikin da-na-sani, Ya kiyaye mu da dukkan zuri’armu.

Za mu sa aya a nan sai sati na gaba idan sarki mai dukka ya kai mu. Ku ci gaba da bin mu cikin mujallar mu mai farin jini, Manhaja.