Tarbiyyar ’ya’ya mata haƙƙin Allah ne akan iyaye

Wannan wani babban al’amari ne da ya tunkaro gidajenmu, wanda ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen tarbitya da addu’a ga ’ya’yansu, musamman ’ya’ya mata.

Ita ƙaruwar gida ba a gidan karuwai ta ke ba, ba kuma zaman kanta take yi ba, a’a hasalima yawancinsu a gaban iyayensu suke, kodai suna jami’a, suna kwana a can ko kuma suna gidan iyayensu.

A baya idan ka ji an ce wance karuwa ce, to za ka same ta a bariki tana sharholiyar ta, ko dai tana shan taba ko wiwi, amman na yanzu cikin zubin ƙarshen zamani, ‘yan mata ne na gida matsakaita waɗanda ba su wuce shekaru 17 zuwa 25 suke zama karuwai.

Yarinya ce za ka ganta Kamila da shigan kamala, babu alaman iskanci tattare da ita, amman ta zubar da kanta, ana lalata da ita a lungun unguwarsu, wata a Hotal, wata a shago, wata a mota, wata a ɗakin uwarta, wata a ɗakin Gayu da ke Off Campus.

Wata karuwar gidan kuma yarinya ce ƙarama ‘yar shekara 14-17 za ta sanya kayan makaranta na Boko ko Islamiyya, amma ba za ta ƙarasa makarantar ba, sai dai ta je a yi zina da ita, ta dawo gidansu ta kwana.

Abin haushi da takaici, wallahi da yawan waxiannan yara babu alaman yunwa tattare da su, kuɗin da ake ba su da yawansu idan ka ga suturar da ke jikinsu, kai ka san sun fi ƙarfin wannan kuɗin.

Abokanmu maza su ke jefa ƙannenmu mata a irin wannan harkar, da zarar sun ga yarinya ta taso, za ka ji suna ce mata ‘yar shila, kamar wata tsuntsuwa, suna zuga ta akan ta yarda tana da kyau, daga nan su ƙulla alaƙa ta hanyar cusa musu ƙawaye karuwan gidan. Ita wannan yarinyar karuwan gidan, a zahiri kamila ce domin ko yan unguwarsu da yawa ba su san tana yi ba, saboda yanayin shigarta na kamala.

Wallahi munin karuwancin gida ya fi na karuwa kilaki mai zaman kanta. Domin da dama sukan je gidan miji da ‘ya’yan wasu, saboda sukan yi ciki a layi ba tare da iyayensu sun sani ba. Mafi yawa daga cikinsu ko da sun yi aure matuƙar sun saba kwaciya da mazaje da yawa, ba su iya jure zama da miji ɗaya.

Mafita a nan ita ce;

  1. Idan kana da ’ya ko ƙanwa ko dai wata mace da kake da iko a kanta, ka tabbatar kana lura da mu’amalarta, suturar da take sanyawa shin kai ka saya mata? Wayar da take riƙewa shin kai ka saya? Turarenta da mai shin kai ka saya? Rashin kulawa da wasu buƙatun wasannan yara da iyaye ke yi, musamman kuɗin kashewa da sayen Data na waya ko ita wayar kanta yakan jefa su wannan harkan.
  2. Dole iyaye su dage da nema wa ‘ya’yansu shiriyar Allah, domin shi ke shiryar da wanda ya so.
  3. Dole ne iyayen da suka saki layin iyaye da kakanni wajen tarbiyyan ‘ya’ya su koma hakan, domin zai yi wuya a baya ka samu yarinya ba a san ina ta ke zuwa ba kuma da su waye ta ke alaƙa kuma waye mai zuwa wajenta, amma na yanzu sun waye za ka ga yarinya har gidansu ta zo da gaye, sai ki ji “Mum ga friend ɗina na School”, Hmp, abu gwanin ban takaici.
  4. Dole iyaye su rage tsangwama, sannan kuma su sanyawa ’ya’yansu wadatar zuciya da nuna musu Allah ke komai, su kuma riƙe mutuncinsu.
  5. A yi ƙoƙari wajen nuna wa yara dogaro da kai, ta hanyar koya musu sana’o’in hannu.

Ubangiji Allah mu ke roƙo ya kare mu daga sharrin zamani, ya kare mana ’yan uwanmu mata daga jin huɗubar Shaidan, duniya da lahira.

Wasiƙa daga IMAM MAHDI, 07066778190.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *