
Daga BELLO A. BABAJI
Dokar ta-ɓaci a Nijeriya ba haye ba ce – gado ce ta iyaye da kakkani, inda wasu ke ganin an fara amfani da ita ne tun a siyasar Nijeriya ta farko a shekarar 1962 lokacin da aka yi zargin an samu manyan kura-kurai a ƙidayar jama’a ta farko da aka fara yi a ƙasar har ta kai ga aukuwar shahararren rikicin nan na kungiyar Action Group (AG) mai tasiri a yammacin Nijeriya.
A ranar 1 ga watan Oktoba, firaministan ƙasar, Sir Abubakar Tafawa-Ɓalewa a wani jawabi da ya yi wa al’ummar ƙasar, ya shaida musu cewa gwamnatinsa tana sane da mugun nufi da wasu ƴan siyasa masu aniyar kifar da halattacciyar gwamnatin dimokuraɗiyyar Nijeriya da ƙarfin tsiya, waɗanda tuni suka fara samun horon soji a ƙasashen waje, don haka ya ƙaƙaba dokar ta-ɓaci.
A ranar 26 ga Oktoba, an tsawaita wannan doka zuwa ga hana tarurrukan jama’a da jerin gwano a ɗaukacin yammacin Nijeriya, inda a ranar 2 ga Nuwamba ne aka zaƙulo wadanda ake tuhuma duka a 1962, irinsu Cif Awolowo da wasu mutane 26 da suka haɗa da Anthony Enahoro, Sam Ikoku, Ayo Adebanjo, Lateef Jakande, Alfred Rewane, J.S. Tarka, Josiah Olawoyin, Dr. Oladipo Maja, Bisi Onabanjo, James Aluko, da dai sauransu, abinda a ƙarshe ya kai ga tilasta wa Gwamnatin Tarayya kafa gwamnatin haɗin-gwiwa.
Tunda ga lokacin ba a sake jin ɗuriyar dokar ta-ɓaci ba sai a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo wanda ya ayyana dokar a ranar 18 ga Mayun shekarar 2004 akan gwamnatin jihar Filato da majalisar dokokinta, wadda rikicin addini da ƙabilanci ya yi dabaibayi wa al’ummar jihar. Kuma gwamnanta Dariye ya kasa kataɓus, Shugaban ya kafa hujja da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wanda ya sahale masa iya ɗaukan irin wannan mataki
Shugaban ya zargi Gwamna Joshua Dariye da gazawa wajen ganin an kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke tsakanin al’ummar Musulmi da Kirista, wanda ya yi sanadiyar rayuka sama da 2,000 tun daga watan Satumban 2001.
Sai Shugaba Goodluck Jonathan, wanda ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomi a Jihohin Borno da Filato a shekarar 2011 kafin daga baya ya faɗaɗa dokar zuwa Jihohin Adamawa da Yobe sakamakon abinda ya kira ta’azzarar rikice-rikicen ta’addanci na Boko Haram a yankin.
A jiya, 18 ga watan Maris, 2025 ne aka kuma, inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi amfani da wannan dama da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi a sashe na 305 na buga gudumar wannan doka a kan Jihar Ribas, wadda rikicin siyasarta ya ƙi ci ya ki cinyewa kusan shekaru biyu da kammala zaɓuka.
Shugaban ya dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da yan majalisar dokoki, waɗanda suka hana jahar kataɓus, har ya buga misali da yadda aka rushe majalisar jahir sukutum kuma aka kasa sake ginawa.
Ga kuma yadda gwamnati da ma wasu mutane masu zaman kansu suka yi iya ƙoƙarin ganin an shawo kan rikicin, amma abin ya ci tura.