Tarihin Hawan Sallah a Ƙasar Hausa (I)

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hawan Sallah wata al’ada ce da ta daɗe a tarihin Masarautun Ƙasar Hausa.

Masarautar Kano:

A wannan masarauta, akwai hawan sallah da ake yi duk shekara a lokacin ƙarama da kuma babbar sallah.

Bayanai na cewa Muhammadu Rumfa ne ya assasa tsarin hawan sallah a Kano. Daga cikinsu akwai Hawan ranar sallah da Hawan Nasarawa da Hawan Ɗorayi da Hawan Daushe da Hawan Fanisau.

Sai dai daga cikin waɗannan haye-haye da ake yi a Masarautar Kano, guda biyu ne suka fi jan hankali.

Hawan Nassarawa:

Yayin wannan hawan, sarki na zuwa gidansa da ke Nassarawa daga nan ya zarce gidan Gwamnati domin yi wa Gwamna gaisuwar Sallah, wanda daga bisani zai fito a kan doki inda zai gamu da cincirindon mutane da ke jiran sa a bakin titi domin yi masa gaisuwa, da kuma ganin wucewarsa da jama’arsa.

Mafi yawan matasa na fitowa domin kallon hawan Sarki na Nassarawa domin kuwa mafi yawan samari da ‘yan mata a wannan lokaci ne suke baje-kolin kwalliyarsu.

Hawan Daushe:

Ana yin wannan hawa ne idan sallah ta kwana biyu da yamma kuma an fara shi ne saboda wani bawan Sarki Muhammadu Rumfa mai suna Daushe da bai samu yin hawan sallah ba, ya ce zai yi masa hawa shi da kansa.
Kuma a wannan hawa, sarki na zuwa ya gaishe da mahaifiyarsa saboda yadda Musulunci ya nuna mahimmancin uwa.

Zagayen da ake yi yayin wannan hawa yana ƙara masa armashi.

Masarautar Haɗeja:

A cewar Jami’in hulɗa da Jama’a na fadar Mai Martaba Sarkin Hadeja, Muhammad Garba Talaki, a Masarautar Hadeja, ana gudanar da hawa iri uku lokacin ƙarama da Babbar sallah.

Hawan Idi:

Ana gudanar da wannan hawa ne bayan sallar Idi da safe.

“Sarki yana hawan, ya zagaya ya gaisa da mutanensa, ya dawo fada ya yi wa jama’ar gari bayani kan abubuwan da suka kamata jama’a su kiyaye da kuma duk saƙon da yake da shi ga al’umma a matsayin saƙon fatan alheri na sallah,” in ji jami’in hulɗa da jama’a na masarautar.

Hawan Bariki:

Shi kuma wannan hawa ana gudanar da shi ne ran biyu ga sallah kuma shi ma kamar Hawan Idi ana yin sa ne da safe.

“Sarki yakan je bariki da shi da hakimansa su gai da DO ‘District Officer’ wanda shi ne a matsayin shugabannin ƙananan hukumomi na wancan lokacin kafin ‘yancin kai.

Hawan Ziyara:

Savanin Hawan Idi da Hawan Bariki da ake gudanar da su da safe, Hawan Ziyara ana yin sa ne da yamma.

A wannan hawan, Sarki yana kai ziyara ne gidan mahaifiyarsa inda zai yi mata gaisuwar sallah.

Hawan Daushe ko Hawan Yara:

Wannan hawan ɗan sarki ne da ‘ya’yan hakimai suke yinsa amma ban da Sarki. Talaki ya ce, “shi ɗan Sarki zai yi hawa tamkar sarki.”

Masarautar Zazzau:

Muhammadu Bello Abdulƙadir Salenken Zazzau, jami’i a Masarautar Zazzau ya ce a wannan masarauta ana gudanar da hawan sallah guda biyu kamar yadda duk sauran Masarautun Ƙasar Hausa ke yi.

Wanda ake yi lokacin shagulgulan ƙaramar sallah da kuma babbar sallah.

A cewarsa, baƙi daga sassa daban-daban na zuwa kallon hawan da ake gudanarwa. Wasu kuma daga ƙauye su ma suna zuwa su sha kallo.

Hawan Idi:

Ana gudanar da wannan hawa ne ranar sallah bayan an kammala sallar Idi.

Sarki da jama’arsa ne suke gudanar da shi kuma mutanen gari suna zuwa domin su sha kallon hawan dawakai.

Hawan Daushe:

A wannan hawan da ake yi da la’asar ɗin biyu ga sallah, mutanen gari da ƙauyukan Zazzau ne suka fi zuwa kallo.

Mutane na zuwa ne domin kallon hawan da kuma al’adun Masarautar.

Hawan Maukibi:

Shi kuma wannan hawan ana yinsa ne don girmama haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) da ake cewa Sallar Gani wato Mauludi.

“Idan an yi sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal akan yi hawa da ake ce masa hawan Maukibi ko hawan Idin Rabi’ul Awwal na Maulidi musamman Daura suna yi,” in ji Salenken Zazzau.

Masarautar Daura:

Alhaji Abubakar Magaji Fada shi ne wakilin Tarihin Daura a wannan Masarauta kuma a cewarsa, ana gudanar da hawa iri uku – hawan sallah qarama, hawan sallah babba da kuma hawan Gani.

A cewarsa, ana gudanar da hawa iri biyu a lokacin ƙaramar sallah da kuma babba:

Hawan Idi:

Kamar kowacce Masarauta a ƙasar Hausa, ita ma Ƙasar Daura tana gudanar da hawa bayan an kammala sallar idi.

Shi ne hawan da ake yi ranar sallah. “Daga masallaci, Sarki na komawa qofar fada.” a cewar Wakilin Tarihin Daura.

Hawan Magajiya:

Shi wannan hawa, mata ‘ya’yan sarauta ne suke yin sa.

“Muna da magajiyoyi a Daura, muna da mayanoni da kuma ita ainihin mai sarautar Magajiya ɗin wanda da can asalin sarautar Daura mata ne suke yin ta.”

A cewarsa, duk da yanzu ba Magajiya ce da mulki ba, amma hawan wata alama ce kan yadda magajiyoyi suka mulki Daura.

“Wannan mata za su taru ‘ya’yan sarauta a gaisa da Sarki, a yi wa’azi na barka da sallah a kawo goron sallah a bayar, sarki kuma ya hau ya zagaye garin Daura ya dawo ƙofar nan ta fada wato kan giwa,”

A wannan hawa, ana samun wakilin gwamnati, za a yi hawa hakimai su kai gaisuwa ga Sarki sannan gwamna ya gabatar da jawabi kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a jihar Katsina.

Masarautar Sarkin Musulmi:

A Masarautar Sarkin Musulmi kuwa, hawa ɗaya ake yi.

Hawan zuwa idi:

A cewar masanin Tarihi a fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Daular Sambo Waliyi Giɗaɗawa, yayin wannan hawan, Sarkin Musulmi yana hawan dawaki da shi da sarakuna su je masallaci.

Ya bayyana cewa “a baya, Turawan mulkin mallaka suna zuwa masallaci su zauna baya ga Musulmi, ana sallah suna kallo,”

“Bayan an ƙare sallah, sarkin Musulmi da Turawa su taho wajen jawabi” inda Sarkin Musulmi ke gabatar da jawabi.

Za mu cigaba a mako na gaba.