Tarihin kasuwanci a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A shekara ta 1453 Miladiyya, a zamanin Sarkin Kano Yakubu ɗan Abdullahi Barja, Sarkin Kano na 16 a mulkin Haɓe, waɗansu Larabawa mutanen Ƙasar Gadamus masu fatauci suka zo daga Tarabulus (Libya), suka sauka a Kano. Sune Larabawan farko da suka fara zuwa kano.

Da saukar waɗannan fatake, sai sukaje wurin sarkin Kano Mallam yakubu, a jujin ’yan Labu, a lokacin ba a gina gidan sarautar Kano na yanzu ba, suka ce da sarki a cikin harshen Larabci su fatake ne, suna so su zauna a Kano domin su yi ciniki.

A wannan lokaci kuwa, limamin Kano Mallam Muhammadu Hashimu ne ya ke fassarawa sarkin Kano abin da waɗannan fataken Larabawa ke faɗa a matsayin tafinta. Daga nan sai sarikin Kano Yakubu ya yi farin ciki ƙwarrai da gaske, sannan ya ce da shamakin Kano ya kai su sararin nan da ke yamma da unguwar Garke watau Dandali, su yi gidaje su zauna a can.

Saboda waɗannan mutane suna da jar fata, sai mutanen Kano suka sa musu suna Turawa. Don haka koda Larabawan suka zauna a wannan wuri, sai mutane suka sanyawa wurin Dandalin Turawa. Dalilin sunan dandalin Turawa kenan yau kusan shekaru 553 kenan.

Tun daga wancan lokaci ne Larabawa suka cigaba da zuwa Kano fatauci. Kamar misali akwai Yamalawa mutanen Yamen, da Larabawan Tunis duk sun riski Kano, amma kowannensu akwai nau’in kasuwancinsu.

Su Larabawan Libya mafi yawan abin da suke sayarwa kayan alatu ne irin na sarakai da kayan kamshi da kayan zaƙi.

Sai dai ya kamata a sani, da wahala ace ga lokacin da aka soma samar da kasuwanci a Kano. A zamanin da, mutanen kano sun fi riƙo da noma fiye da wata harkar kasuwa, amma ana aiwatar da sana’o’i na gargajiya misalin rini, jima, ƙira da saƙa. Waɗannan su suka haifar da ainihin kasuwanci, domin mutum zai yi abu ya sayar ga jama’a.

Koda ya ke, a wancan lokacin, ba a fara amfani da kuɗi ba a Kano, ana yin cinikin furfure ne, watu ban gishiri in ba ka manda.

Daga baya ne lokacin da fatake Larabawa ko Asbinawa da Agalawa suka zo Kano, kasuwanci ya fara kankama a Kano.

Haka ma, sauyawar akalar kasuwancin ƙasar Hausa daga izuwa Kano kamar yadda littafin ‘Kano civil war and the British Ober Rule 1882-1940’ na Muhammad F.A ya ruwaito ya taimakawa Kano matuƙa gaya, domin an samu cewar fatake sun yi wa Katsina tawaye ne, suka koma Kano ungurungum da kasuwancinsu.

Zuwan Turawa Kano kuwa, da kuma yadda suka samar da farin kuɗi a shekara ta 1930 don yin musanje ya haɓaka kasuwanci sosai a Kano. Domin a zamanin ne Kanawa suka samu buɗewar ido ainun a harkar, har ya zamana suna yiwa kansu jagoranci, abin da ya sanya Kano ta ƙara bunƙasa kuma kenan har ake ma ta kirari da Tumbin giwa ko da me kazo an fika.

Kai ba ma nan ba, har daga ƙasashen Kasabalanka ta Morocco da Yunana ta Girka fararen fata sun zo fatauci Kano, bari kuma ku ji yadda su ka zo.

A ƙarni na goma sha biyar, zamanin mulkin Sarkin Kano Muhammdu Rumfa, wasu Turawa fatake sun zo Kano daga girka. Ƙasarsu a can kusa da Istanbul ta ke, ana kiranta Yunana, a yankin ƙasashen Turawa.

Su waɗannan Turawa sun zo Kano ne domin fatauci, sun kai kimanin arba’in, da raƙuma kusan talatin da biyar, masu ɗauke da kayayyakin dukiyoyi masu yawa kamar su alkyabbu, jabbobi, falmarori, kuftoci, jauhohi, hulunan dara, takalma, kilisai, takardu da kuma takubba.

Sai waɗannan fatake suka iso ƙofar fadar sarki, suka nemi iso sannan suka yi gaisuwa gare shi da Larabci. A cikin malaman da su ke zaune, sai wani Malami mai suna Abdurrahman ya riƙa fassara maganarsu da Hausa.
Daga nan sai waɗannan fataken suka gayawa sarki Muhammadu Rumfa cewa su ba Larabawa ba ne, Turawa ne mutanen Giris. Sun iya larabci ne kurum kuma fatauci ne ya kawosu kano. Nan ta ke sai suka fito da kayayyakin da su ke sayarwa.

Da ya ke a wannan zamanin, ba a soma ciniki da kuɗi ba, sai sarkin na Kano ya tambaye su cewa ku kuma me kuke da buƙatar saye a wurinmu? Sai suka ce muna buƙatar bayi, fatu, kiraga, albasa da tafarnuwa. Daga nan sai sarki ya ce yana buƙatar dukkanin kayayyakin nasu, sannan yasa a shirya musu kayayyakin da suke da buƙata.

An ce, an ba su masauki a inda asbitin unguwar Marmara ya ke a yanzu, aka yi musu ɗakuna dogaye da tsangayu masu faɗi da tsawo, aka yi musu hayin shirayi, sannan kowanensu aka ba shi gado da tabarma.

Sarki ya tura musu bayi domin su yi musu hidima. A lokacin sai da bayin suka haka musu tijiya domin samar musu da ruwa saboda rashinsa, shi ne har aka ce idan Turawan suna buƙatar ruwa sai su ce Akwa, wai sunan ruwa kenan da yarensu, daga bisani sai aka sanyawa rijiyar suna ’Yar Akwa.

Waɗannan Turawa da suka zo a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, su ne suka fara kawo takardu da takobi. Suna kiran takardu ‘Yarta krata’, takobi kuma ‘Takopis’. Wataƙila daga nan sunayen suka samo asali domin da harshen Hausa kansakali ake kiran takobi.

Da lokacin tashin fataken ya yi, sai suka haɗa gagarumar kyauta suka bai wa sarki, sarki ya ɗauki nasa ya kuma rarrabawa hakimansa, sannan ya sa aka ba su bayi hamsin mata da maza, da dawaki masu yawa, gami da sauran kayayyakin da suka buƙata tunda fari, sannan aka haɗa tawaga domin ta yi musu rakiya.

Su ka fita daga ƙasar Kano, suka bi ta wani gari mai suna Dingas zuwa Damagaran, suka kalli hanyar Tunis, suka shiga cikin sahara har zuwa wani gari mai nisan gaske da ke cikin sahara a yankin Libya, sunansa Murzuk, daga nan suka dangana da birnin Turawa a bakin babban tekun bahar Rum, suka shiga manyan jiragen ruwa, suka koma ƙasarsu ta girka. Waɗannan sune Turawan farko da suka soma zuwa Kano.