Tarihin Mada Garin Aliyu Babba Ɗan Malam Muhammadu Sambo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD

Asalin su Fulani ne da suka fito daga yankin Ningi ta Jihar Bauchi da zummar za su kai caffa a wajen Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo Tagammadahullahu birahamatihi a Sakkwato domin shiga dumu-dumu a cikin jihadin jaddada addinin Musulunci wanda Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo ya jagoranta.

Sun zauna a wurare da dama kamar Ƙiru da Gwarzo (da ke Jihar Kano ta yau) da Matazu da Fawwa ( dake Jihar Katsina a halin yanzu) da kuma Wonaka da ke Jihar Zamfara ta yanzu, kafin daga bisani Malam Muhammadu Sambo ya jagorance su ya zuwa inda suke a halin yanzu.

Malam Muhammadu Sambo ya samu cika gurin/burin shi na taimaka wa Mujaddadi a fagen jihadin jaddada addinin Musulunci domin kuwa ya yi wafati ne a ɗaya daga cikin yaƙe-yaƙen da Mujahiddai suka fafata da abokan gaba, shi da ɗan shi Aliyu ƙarami. Ana kyautata zaton a Yaqin Alwasa ne suka yi shahada.

Daga cikin ɗiyan Malam Muhammadu Sambo su uku (Aliyu Babba, Aliyu Ƙarami da Amadu) Aliyu Babba ne ya soma sarautar wannan gari na Mada daga shekarar 1823 zuwa shekarar 1849 da laƙabin sarautar ‘Magaji’ wanda kuma da shi ne ake kiran duk wanda ya yi sarauta a Mada ya zuwa yau.

Bayan shi an yi sarakuna guda uku daga zuriyar shi, har zuwa shekarar 1940 lokacin da sarautar ta ɗan tafi yawo har sai zuwa shekarar 1972, lokacin da Allah ya dawo da ita ta hannun Magaji Sama’ila ɗan Alhaji Barau na yanzu.

Sarakunan kuma sune; Magaji Isiyaku wanda shi ne ya gade/gaje shi a shekarar 1849 zuwa shekarar 1866, Magaji Hamza 1866-1890 da kuma Magaji Giɗaɗo wanda aka fi sani da Giɗe Makaho 1890-1940.

Tsakanin 1940 zuwa 1972 da sarautar ta fita daga gidan Magaji Aliyu Babba ɗan Malam Muhammadu Sambo, an yi sarakuna guda biyar kamar haka; Magaji Bawa 1940-1943, Magaji Taula 1943-1949, Magaji Atu 1949- 1954, Magaji Bello Amadu Sakkwato 1954 – 1972, Magaji Bara’u Isa wanda ya yi wata uku a cikin shekarar 1972 lokacin da aka dawo da sarautar a gidanta na asali ta hannun Mai girma Magaji Sama’ila Alhaji Barau na yanzu.

“Sha labari giye mai Mada sai na zo ga Magajin Mada,” inji makaɗi Buwai Shemori daga cikin waƙar da ya yi wa Alhaji Sama’ila ɗan Alhaji Barau ɗan Magaji Hamza, ɗan Magaji Isiyaku, ɗan Magaji Aliyu Babba, ɗan Malam Muhammadu Sambo a lokacin da aka naɗa shi a shekarar 1972, a matsayin Magajin Mada na 5 daga wannan zuriya ta Malam Muhammadu Sambo, kuma Magajin Mada na 10 tun kafuwar wannan gari.

An haifi Magajin Mada, Alhaji Sama’ila a shekarar da Mai girma Sardaunan Sakkwato, Alhaji Abubakar ɗan Modibbo Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu’azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo ya zamo Sarkin Musulmi, watau 1938 a garin Hayin Alhaji da ke cikin Masarautar Tsafe ta yanzu. Wannan gari , Alhaji Barau mahaifin Magaji Sama’ila ne ya ƙirƙire shi, shi ne ma dalilin da ake kiran garin da sunan shi, watau ‘Hayin Alhaji’.

Ya fara karatun sa na addinin musulunci a wajen Kawunsa/Baffansa a gidan Liman Na- Wonaka domin daga nan ne mahaifiyarsa ta fito.

Magaji Sama’ila ya tafi Kano inda ya zurfafa iliminsa na addini ya kuma koyo sana’ar hannu ta ɗinkin tela da kuma yaƙi da jahilci a fannin karatun zamani.

Bayan ya dawo gida Hayin Alhaji ya ci gaba da rayuwarsa har zuwa shekarar 1961, lokacin da Magajin Mada, Bello Amadu Sakkwato ya nemi ya dawo gida domin ya riƙa masa gudanar da sha’anin mulki. Ya naɗa sa mai kula da wata Unguwa da ke cikin garin Mada da ake kira ‘Shiyar Sarkin Yaƙi’ da laƙabin Sarkin Yaƙi.

Biyayyarsa da ɗa’a da kwantata gaskiya da hankali da son jama’a da kuma takatsantsan ɗinsa ne ya sanya aminci sosai tsakaninsa da Magaji Bello Amadu Sakkwato da al’ummar Ƙasar Mada kwata.

A ƙarshen mulkin Magaji Bello Amadu Sakkwato ne a shekarar 1972 aka sake turo Malam Bara’u Isa (daga wajen zuriyar Magaji Aliyu Babba ɗan Malam Muhammadu Sambo) domin ya mulki wannan gari/ƙasa ta Mada. Ya na da wata 3 a wannan matsayi ne mutanen ƙasar suka nemi mulki ya dawo gidansa na asali ta hanyar kai koke a Majalisar mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III a Sakkwato.

Bayan gudanar da bincike da kammala shawara akan wannan ƙorafi ne, Mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ya umurci masu zaɓen sarki na Ƙasar Mada dasu zavo wanda ya dace daga cikin zuriyar Magaji Aliyu Babba ɗan Malam Muhammadu Sambo domin a naɗa sa wannan matsayi na Magajin Mada. Allah cikin ikonsa ya baiwa Sarkin Yaƙi, Alhaji Sama’ila ɗan Alhaji Barau ɗan Magaji Hamza ɗan Magaji Isiyaku ɗan Magaji Aliyu Babba ɗan Malam Muhammadu Sambo wannan matsayi, aka kuma naɗa sa ranar 22/8/1972.

Daga wannan lokaci ya zuwa yau, Magajin Mada Alhaji Sama’ila ɗan Alhaji Barau ya shafe shekaru 50 kenan akan karagar mulki tare da kawo wa wannan ƙasa abubuwan ci gaba na zamani ta hanyar sadaukar da kansa da yayi tare da haɗa kan al’ummarsa domin ganin an samu wannan ci gaba mai ma’ana.

Allah ya jiqan magabatanmu, ya ƙara taimakon Mai girma Magajin Mada/Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Mada da ke Masarautar Gusau a Jihar Zamfara, Amin.

(Ɗanmadamin Birnin Magaji) [email protected]
+234 814 938 8452.