Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Sarki Muhammadu Abbas shi ne sarki na 51 a jerin sarakunan Kano, sannan kuma sarki na 9 a jerin sarakunan Fulani, har wayau kuma shi ne sarki na farko da Turawa suka fara naɗawa.
Sarki Muhammadu Abbas mutum ne jarumi, kuma mai faɗa ba fasawa ko kuma ana iya cewa mutum ne kaifi ɗaya. Ya kasance sarki mai haƙuri da jama’arsa.
Sarki Abbas ya yi mulki tare da Turawa, saboda haka hakimansa suka samu dama ta dalilin haƙurinsa da kawaicinsa suna iya yin magana kai tsaye da Turawa, har sai da ta kai jallin munafurci ya fara gudana a tsakanin Turawannan da wasu daga cikin hakiman sarki Abbas. Irin wannan lamari na tsaka da faruwa sai Allah ya kawo wani Bature mai suna Mr. Temple, shi ya takawa wannan al’ada burki. Ya samar da kyakkyawan tsari, ya yankawa sarakuna da sauran ma’aika albashi.
A zamanin sarki Abbas ne aka yi wani gagarumin taron sarakuna, gabas da yamma, kudu da arewa a cikin shekarar 1912. A zamanin sarki Abbas ne aka gina wasu kasuwanni a Kano. Sannan kuma a zamaninsa ne a ciki shekarar 1910 aka gina wata makaranta a cikin Nassarawa wacce a yanzu ta koma gidan ɗanhausa.
Sarki Muhammadu Abbas ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara goma sha shida. Ya rasu a shekarar 1919. An binne shi a gidansa da ke Nassarawa.
An haifi Abbas a cikin shekarar 1856, a cikin gidan sarautar Kano, a lokacin mahaifin Abdullahi Maje Karofi, yana da shekara ɗaya kacal a gadon Sarauta.
Abbas ya kasance lokacin mahaifinsa ya zaukin tsawon lokaci bai riƙe da wata sarauta, saboda kana nan shekarunsa.
Haka ma dai Abbas, ya zauna zamanin mahaifinsa ba tare da ya riƙe wata sarautaba. Sai a zamanin ƙaninsa Aliyu Babba, aka ba shi sarautar, Sarkin Dawakin Tsakar gida. Ba a ɗauki tsawon lokaci ba kuma aka masa ƙarin girma, ya zama Wamban Kano.
Lokacin da Turawan mulkin Mallaka suka mamaye birnin Kano. Wambai Abbas, yana tare da tawagar Sarki Aliyu Babba a Sokoto.
Aliyu Babba, da tawargarsa sun kwashe kwanaki a Sakkwato a wancan lokacin. Sun kaima sabon Sarkin Musulmi, Attahiru Ahmadu 1, ziyarar taya murna. Bayan an tafka muhawura zazzafa, akan cewa hijira, za a yi kokuwa, za a zauna ƙarƙashin Turawan Mulkin Mallakane? Aliyu Babba, ya kamo hanyar komawa gida. Bayan isowarsa birnin Goga, ya samu labarin faɗuwar Kano, sai ya yanke shawarar yin hijira. Ya kuma kama gabansa yai tafiyarsa. Jama’arsa suka dawo ƙarƙashin Wambai Abbas, suka kuma kasance cikin wani yanayi na ruɗani, da rashin sanin yadda za su yi. Nan-da-nan Wambai Abbas, ya tattara kan mutane ya jawo hankalinsu, da nuna musu mafita.
Mafitar kawai itace su yi taƙiya, su ɓoye imaninsu a lokacin. Wambai Abbas, ya nuna musu haɗarin, tunkaran Turawan mulkin mallaka, a bakin daga. Fiye da mutum 10,000, suka yadda da Wambai Abbas, suka yanke shawaran su ba za su yi hijira ba, kuma ba za su yi yaƙi ba. Za su koma Kano, su nemi sulhu, matuƙar za a barsu su yi addininsu. Wambai Abbas, ya shigo garin Kano, ranar 7, ga watan march (1903).
Ya kuma shigo ne ta ƙofar Kansakali. Gwamna Lugard, da kansa ya sa aka kira Wambai Abbas, inda ya umarce shi da cewar ya miƙa dukkan maƙamansa. A kuma ranar 7, ga watanne Lugard, yana da Wambai Abbas, muƙaddas, Wamda zai kula da masautar Kano. Saboda lokacin da Aliyu Babba, zai tafi Sokoto, yatattara masu sarautar Kano kacokaf, suka nufi Sokoto. San Kurmi, shi ne kaɗai mai riƙe da babbar sarauta wanda aka bari a Kano. A wannan lokacin Kano taso ta sake faɗawa matsala domin ɗan Sarki Tukur, Abdu Lele, wanda yana ɗaya daga cikin mutanen, da suka taimakawa Tuwara, wurin murƙushe Kano, ya nemi, a sakamai da sarautar Kano. Amma buƙatae Abdu Lele ba ta samu biya ba domin al’umma sun koka sun ce ba zai yi adalci ba sam.
Bayan Gwamna Lugard, ya ga yadda Wambai Abbas, ya amsu ga jama’arsa, sai ya yanke shawarar naɗa shi sarautar Lano, ya tashi daga fagin muƙaddas, ranar 3, ga watan April 1903. Daga wannan lokacin ne naɗa sarauta ya koma hannun Turawan mulkin Mallaka, maimakon fadar sarkin Musulmi.
Bayan sarki ya zauna kan karagan mulki ne ya fara naɗe-naɗen, sarautu. Cikinsu ya naɗa ɗansa Abdullahi Bayero Ciroman Kano. Abbas, yarasu yana ɗan shekaru 63, ranar juma’a 1, gawatan March 1919. Yabar yara 18, kamar haka. 1 Abdullahi Bayero, 2. Abdulkadir, 3 Muhammadu Inuwa, 4. Hashim, 5. Ibrahim Cigari, 6. Yusifu, 7. Isan Nasarawa, 8. Bashar, 9. Shehu, 10. Garba, 11. Hamidu, 12. Sani, 13. Isan Panisau, 14. Ahmad Tijjani, 15. Hassan, 16. Badayi, 17. Muhammadu, 18. Zubairu. Littafin da muka dogara da shi Abdullahi Bayero.