Taron APC: Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga ’yan jam’iyyar APC

Ya ku dattawanmu na APC, mun rubuta wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa ce, don buƙatar a gudanar da al’amura masu matuƙar muhimmanci tare da neman gyara a siyasa a babban taron jam’iyyarmu ta APC mai zuwa. Ya ku dattawanmu na jam’iyyar, mu ’Yan Ƙungiyar Masu Son Cigban APC (CAY), mu ba a haife mu a matsayin ma’asumai a siyasa ba, don haka za mu so mu bi ku da cikakken ladabi.

Kafin mu cigaba da yin rubutu akan wannan batu, za mu so mu bayyana cewa, ƙungiyar matasa masu kishin APC, wacce a ƙarƙashinta mu ke rubuta wannan wasiƙa, za ta cigaba da zama gungun matasan masu damuwa da kare mutunci da al’adar babbar jam’iyyarmu ta APC.

Kuma a matsayinmu na matasa masu son cigaban wannan babbar jam’iyya, babu abin da ke karya mana zuciya kamar irin yadda ake cigaba da gudanar da siyasar da mu ke gani kan zaɓe a jam’iyyarmu, musamman na kujerar shugaban ƙasa, wanda a ganinmu ya kamata kowa ya yanke shawara cikin sauƙi ya kuma duba waɗanda su ka fi cancanta su yi takara, domin kuwa Hausawa na cewa ‘ido ba mudu ba, amma ya san kima’.

Abin baƙin ciki ne da damuwa ganin yadda wani dattijon da ya ke da ƙima a jam’iyyarmu, amma yanzu mu ka kasa gane kan gadonsa, kuma mutum mai daraja a jam’iyyar ya rikiɗe ya zama wakili na kamfen ɗin ɓatanci – duk don son kai na siyasa. Tabbatacciyar hujja ce cewa, APC na cikin ruɗani.

Kamar yadda ɗaya daga cikin dattawan yankin Kudu maso Yamma ya bayyana a kwanakin baya a wata hira da aka yi da shi cewa, “jam’iyyarmu mai girma ta APC ta faɗa cikin rikici, wanda idan ba a yi gaggawar magance ta ba za ta iya kai wa ga halaka. Mafi muni kuma, rashin zaman lafiya a jam’iyyar APC na iya dagula ɗimbin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta tare da zama babbar matsala ga shugabanci ko zaɓen 2023.

“Dalilin rikice-rikicen da ke faruwa a yanzu ya samo asali ne daga muradin ’yan jam’iyyar da dama da suka fara da babban taron jam’iyyar APC mai zuwa. Kuma a fayyace babu laifi idan mutane suna da buqara, abin da ke da haɗari shi ne jefa jam’iyyar cikin ruɗu ga burin mutum.”

Taƙaitaccen bayanin da ke sama ya bayyana halin da jam’iyyar ta ke ciki. Kowa na son ya zama mai jan ragamar harkokin jam’iyya, hatta waɗanda ba su da alaqa da shugabancin jam’iyya. Kuma duk mun san waɗanda za su iya yin aikin da waɗanda ba za su iya ba. Da manya su kawar da burinsu su goyi bayan ɗan takarar da ya dace, sun gwammace su zaɓi ɓata wa juna suna a kafafen yaɗa labarai domin neman babban kujera a jam’iyyar.

Babu wani misali da ya bayyana waɗannan iƙirari kamar abubuwan da suka faru a ’yan makonnin da suka gabata, inda ɗan takara na gaba-gaba a takarar shugabancin jam’iyyar, mutumin da bai taɓa faɗuwa zaɓe ba cikin shekaru 44, mutum ne mai mutunci da riƙon amana, mutumin da kasance maginin gada kuma shugaban jam’iyya na gaskiy, amma ’yan jam’iyyarsa na zargin sa da tarin ƙarya.

APC na buƙatar ceto, jam’iyyar na buƙatar fansa, jam’iyyar ta cancanci daidaito da riƙon amana.

Jam’iyyar tana buƙatar aiki tare da jagoranci na haɗin kai, sannan kuma sama da komai, jam’iyyar na buƙatar kwanciyar hankali kuma babu wanda ya fi kowa kawowa ko bayar da waɗannan abubuwa duka sai tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma sanata mai ci, Sanata Abdullahi Adamu (Turakin Keffi).

Ya ku dattawanmu, ba mu na cewa, ba daidai ba ne duk wani dattijon jam’iyya ya fito ya nemi wani muqami a jam’iyyar APC – walau Sanata Adamu ko wani mutum da tsarin mulki ya ba shi damar neman muƙamin zaɓe. Kuma mu na ganin ya na da kyau ko ma wane ne daga jam’iyyar na da kamar fitowa, don neman muqaman jam’iyya cikin tsari, gaskiya da adalci.

Amma idan ɗan takara mafi girma, wanda tarihinsa da amincinsa ya wuce kowa, wanda ya yi nasara a siyasance kuma babban mai ginin gada, shugaban da zai kawo jituwa, haɗin kai da cigaba ga jam’iyyar musamman a lokacin da ake tunkarar zaɓen 2023 ya fito neman kujera, adalci ne kuma ya dace duk ɗan jam’iyyar APC mai tunani ya goyi bayan manufarsa.

Sanata Abdullahi Adamu a matsayinsa na uban jam’iyyar da kansa, ya fahimci ƙa’idoji da tsare-tsare da tsarin mulkin jam’iyyar da kuma sanin ƙa’idoji da al’adun da aka gina a lokacin kafa jam’iyyar. Irin wannan mutum ne kawai zai tabbatar da zaman lafiya da cigaba ga babbar jam’iyyarmu.

Akan wannan batu mu na kira ga dukkan mambobi da dattawa da matasa da mata na babbar jam’iyyarmu da su gaggauta bai wa Sanata Abdullahi Adamu goyon baya a matsayin mai gada mai kyau da cigaba na APC ya zo 2023 da kuma bayan. Babu lokaci kuma babu wuri don ra’ayi – matakin yanke shawararmu ya kamata ya zama cancanta, yarda da girmamawa ya zo 26 ga Maris.

Mun gode da lokacinku dattawanmu!
Allah ya taimaki APC!
Allah ya albarkaci Tarayyar Nijeriya!

Daga Matasa Masu Kishin Jam’iyyar APC (CAY)