Taron APC: Sanata Abdullahi ya fi dacewa da shugabancin jam’iyya – Masu ruwa da tsaki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gabanin babban taron jam’iyyar APC mai mulki a ranar 26 ga Maris, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun jaddada goyon bayansu ga ɗan takarar shugabancin jam’iyyar kuma tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu.

Ƙungiyar wacce ta ƙunshi dattawan jam’iyyar na yanzu da kuma tsoffin ’yan majalisar APC da na yanzu, da na tsohuwar jam’iyyar da kuma matasan jam’iyyar a faɗin jihohi 36 na tarayya, sun ce ya zama wajibi a bayyana matsayinsu da ranar da za a yi zaɓe, gabanin kusantowar taron.

Da ya ke zantawa da wasu zaɓaɓɓun manema labarai, shugaban ƙungiyar kuma tsohon ɗan majalisa a jihar Adamawa, Injiniya Adamu Auta Fufure ya ce, abin da jam’iyyar APC ke buƙata a yanzu shi ne mutum irin Sanata Abdullahi, wanda ya fahimci jam’iyyar kuma ’ya’yan jam’iyyar suna mutunta shi sosai.

“Shi ɗan takarar siyasa ne kuma babban jagora, kuma abin da jam’iyyar ke buƙata ke nan a yanzu.”

Fufure ya qara da cewa, Sanata Adamu shi ne shugaban da zai kawo jituwa, haɗin kai da cigaba ga jam’iyyar musamman a lokacin da muke tunkarar zaɓen 2023.

Shi ma Sani Baba Kano, ya ce, farin jini da karɓuwar da Sanata Adamu ya samu ya nuna cewa shi ɗan jam’iyya ne na gaskiya, wanda ya yi ƙoƙarin kawo zaman lafiya da cigaban jam’iyyar APC da kuma kowace jam’iyyar da ya ke a cikin shekaru arba’in da suka gabata.

“Mutane ƙalilan ne suka ba da gudunmawar cigaban ƙasar nan da cigaban jam’iyyar kamar yadda Sanata Abdullahi Adamu ya yi. Ni kaina, ina jin waɗanda ke adawa da burinsa na zama shugaban ƙasa, mutane ne da ba su da wata maslaha ga jam’iyya a zuci”.

A nata ɓangaren, Evelyn Johnson daga jihar Akwa Ibom kuma tsohuwar shugabar mata ta bayyana cewa mai neman tsayawa takarar yana mutunta duk wani mutum da kuma bin qa’idojin dimokuraɗiyya da aka sani kuma shi jagora ne na gaskiya.

Wani Shugaban Matasan Jam’iyyar APC daga Jihar Oyo, Bamidele Lekan Martins ya ce, “ban taɓa haɗuwa da Sanata Abdullahi Adamu ba, kuma ban tava yi masa magana ko na kusa da shi ba game da burinsa na zama Shugaban ƙasa amma ga duk mai ƙaunar APC, mun san cewa Sanata Abdullahi Adamu shi ne mutumin da ya fi dacewa da wannan aiki.”