Taron fidda gwani: Osinbajo bai ce zai ba wa daliget masauki a Abuja ba – Ƙungiya

Daga IBRAHIM HAMZA MUHAMMAD

Kwamitin Sadarwa na Ƙungiyar yaƙin neman takarar shugaban ƙasa ta mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ta ce an yi mata ƙagen cewa wai ta ce Osinbajon zai sama wa wakilan Jam’iyar APC (daliget) 7,000 masaukai a otel-otel a Abuja yayin taron fidda gwani na Jam’iyar APC.

Wannan ya biyo bayan alaƙantata labarin ƙarya da aka yi na cewa wai mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ne ya furta hakan.

Sanarwar da ta fito daga kwamitin ta ci gaba da cewa, “Mun ga wani labari na ƙanzon kurege da ya ce wai kwamitin yaƙin neman zaven Osinbajo ya ce zai samar da ɗakunan otel-otel har guda dubu bakwai (7000) ga wakilai”.

A cewar ƙungiyar: “Zuƙi ta mallen ta ruwaitu cewa, an alaƙanta cewa wai Mataimakin na musamman ga mataimakin Shugaban ƙasar, Sanata Babafemi Ojudu ne wai ya shaida wa wakilan jam’iyya haka a Minna, a lokacin da yake zawarcin da a zaɓi Osinbajo yayin zaɓen 2023.”

Sanarwar ta musanta cewa, Sanata Babajide Ojudu bai faɗi haka ba, kuma kwata-kwata babu wannan shirin na samar da ɗakuna da abinci ga wakilai, don ƙarya ce tsagwaronta.

Kwamitin ya jaddada cewa, Farfesa Yemi Osinbajo yana ci gaba da ganawa da wakilan jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki a jihohi, tare da amsa tambayoyinsu game da siyasa da jagoranci.

Sanarwar ta ƙara da cewa, babban burin Kwamitin shi ne cigaba da ganawa da ‘yan Jam’iyyar APC da kuma burin ganin an tunkuɗa ƙasar Nijeriya zuwa gaba bayan zaɓe mai zuwa na 2023.