Taruka biyu na Sin na da babbar ma’ana ga al’ummun duniya

Daga AHMAD FAGAM

Yayin da a ƙarshen mako aka ƙaddamar da manyan taruka biyu na ƙasar Sin na shekara-shekara, wato taro na 5 na majalisar wakilan jama’ar ƙasa NPC karo na 13, da na kwamitin hukumar bada shawara kan al’amurran siyasar ƙasar Sin CPPCC, dake gudana a birnin Beijing, wasu kafofin watsa labaran ƙasa da ƙasa sun bayyana tarukan a matsayin masu matuƙar muhimmanci ba kawai ga ƙasar Sin ba, har ma da alummar duniya baki ɗaya.

Kamfanin watsa labarai na ƙasar Kenya wato KBC yana da irin wannan ra’ayi, inda ya gabatar da wani sharhi dake nuna cewa, tarukan biyu na ƙasar Sin waɗanda ke gudana a birnin Beijing na ƙasar suna jawo hankalin al’ummun ƙasashen duniya matuka, musamman ma batun dake shafar shawarar “ziri ɗaya da hanya ɗaya”, saboda shawarar tana amfanar dukkan duniya, har ma tana taka muhimmiyar rawa wajen cuɗanyar tattalin arzikin duniya. Sharhin ya ƙara cewa, ƙasar Sin abokiyar cinikayya mafi girma ce ta ƙasashen Afirka, wadda ke zuba jari mafi yawa a nahiyar, musamman ma cikin ’yan shekarun da suka gabata, ƙasashen Afirka suna cin gajiya daga jarin da ƙasar Sin ke zubawa a nahiyar, misali a ɓangarorin manyan ayyukan gina kayayyakin more rayuwar jama’a da fannin kiwon lafiya.

Don haka batutuwan da za a tattauna yayin tarukan biyu na ƙasar Sin suna da babbar ma’ana ga ƙasashen Afirka. Ban da haka, shugabannin ƙasashen Afirka da dama suna sa ran za su kara kyautata hulɗar dake tsakanin ƙasashensu da ƙasar Sin, tare kuma da ƙara karfafa haɗin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

Bugu da ƙari, ita ma jaridar “Observer” ta ƙasar Pakistan, ta wallafa wani sharhi a ranar 4 ga wata, inda aka bayyana cewa, ƙasar Sin ta samu amincewa daga masu zuba jari a faɗin duniya, bisa salon ƙaruwar tattalin arzikinta na cigaba mai dorewa, yanzu haka ana gudanar da taruka biyu a ƙasar Sin, inda ake tabbatar da cewa, idan ƙasar Sin ta ci gaba da samun wadata, tabbas ne daukacin ƙasashen duniya za su ci gajiya daga ci gaban ƙasar ta Sin. Haƙiƙa, dukkan manufofin raya tattalin arziki da cigaban alumma da ƙasar Sin ke aiwatarwa suna taka muhimmiyar rawa ga cigaban tattalin arzikin duniya.

Alal misali, a cikin rahoton da hukumar ƙididdiga ta ƙasar Sin ta gabatar na baya bayan nan kan ci gaban ƙasar Sin a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasa a shekarar 2021, rahoton ya ce, duk da ƙalubaloli da dama da ake fuskanta a ciki da wajen ƙasar Sin ta fuskar tattalin arziki, amma ƙasar Sin ta samu karuwar tattalin arziki da kaso 8.1 bisa 100, kana yawan ci gaban tattalin arzikin ƙasar Sin ya ƙara babban kuzari kan tattalin arzikin duniya wanda ake fadi-tashin farfaɗowarsa, sannan tattalin arzikin ƙasar Sin yana mara wa tattalin arzikin duniya baya matuka.

A shekarar 2021, gudummawar da ƙasar Sin ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya ta kai kaso 25 cikin 100. Jimilar kuɗaɗen shigi da ficin kayayyaki ya kai kuɗin Sin Yuan triliyan 39.1 a ƙasar Sin, wanda ya ƙaru da kaso 21.4 cikin ɗari bisa makamancin lokacin na shekarar 2020, don haka ƙasar Sin ta shafe shekaru 5 a jere tana zama ta farko a duniya a fannin cinikin kayayyaki. Hakan ya nuna cewa, ƙasashen duniya na buƙatar kayayyaki ƙirar ƙasar Sin. Al’ummar ƙasar Sin na sayen kayayyaki daga sassa daban daban na duniya, abin da ke nuna ƙarin buƙatunsu.

Dama dai batun ɓullo da dabarun kyautata yanayin tattalin arzikin ƙasa na daga cikin muhimman ajandojin manyan tarukan shekara-shekara na ƙasar Sin, don haka babu tantama duniya zata ci gaba da cin gajiyar ƙudurorin dake kumshe a tarukan na bana.