Tashar ruwan ciniki cikin ‘yanci ta Hainan ta shaida ƙaruwar buɗe ƙofa ta ƙasar Sin ga ƙasashen waje

Daga CMG HAUSA

“Ba za a rufe ƙofar da aka buɗe ba, maimakon haka za a kara buɗewa”, wannan shi ne babban alƙawarin da ƙasar Sin ta ɗauka ga duniya. Ci gaban da aka samu na gina tashar ruwan ciniki cikin ‘yanci ta Hainan a cikin shekaru huɗu da suka gabata, ya zama wani misali na ƙudurin ƙasar Sin na cika alƙawuran da ta dauka.

A ranar 12 ga watan Afrilu, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, wanda ke ziyarar aiki a lardin Hainan, ya ziyarci yankin raya tattalin arziki na Yangpu, don fahimtar yadda yankin ke samun bunƙasuwa, inda aka gina tashar ciniki cikin ‘yanci da ke da salon musamman na ƙasar Sin.

Tashar jiragen ruwa ta ciniki cikin ‘yanci, ta nuna matsayi mafi girma game da buɗe ƙofa ga ƙasashen waje a yanzu haka. A ranar 13 ga watan Afrilu na shekarar 2018, aka soma aikin gina tashar ciniki cikin ‘yanci mai salon ƙasar Sin a Hainan.

KARANTA: Li Keqiang: Sin za ta rungumi salon cigaba bisa daidaito a fannin cinikayyar waje

A cikin shekaru huɗu da suka gabata, yawan adadin kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, bisa manufar “Kawar da haraji baki ɗaya” na tashar ya zarce yuan biliyan 7, kuma matsakaicin karuwar yawan jarin waje da ake amfani da shi a duk shekara ya kai kashi 79.4%, kana an aiwatar da manufofi fiye da 150, game da tashar ciniki cikin ‘yancin da dai sauransu.

Waɗannan nasarorin da aka samu sun shaida yadda ƙasar Sin ta ƙuduri aniyar fadada buɗe kofa ga waje, da kokarin samun nasara tare da sauran ƙasashen duniya.

Lokacin da aka fi shan wahala, kamata ya yi mu ƙara buɗe kofa. A cikin shekaru huɗun da suka gabata, duk da fuskantar ƙalubale da dama, ciki har da yaɗuwar COVID-19, da yaƙi da tsarin dunƙulewar tattalin arzikin duniya da dai makamatansu, ƙasar Sin tana sa ƙadimi ga aikin gina tashar ciniki cikin ‘yanci bisa shirin da ta tsara.

A ranar 1 ga watan Janairun bana, aka fara aiki da yarjejeniyar abokantaka kan tattalin arziki na yankin (RCEP), inda aka yi hasashen cewa, tun daga Hainan har zuwa ƙasar Sin baƙi ɗaya, wani sabon zagaye na buɗe kofa ga ƙasashen waje zai bai wa duniya damar raba damammaki daga dukkan fannoni, kana da ba da kuzarin da ake bukata wajen farfaɗowar tattalin arzikin duniya.

Mai fassara: Bilkisu Xin