Tashin farashin baƙin mai da canji sun jawo min naƙasu a kasuwancina – Obasanjo

Daga AMINA YUSUF ALI

Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya a Jamhuriya ta biyu, Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda tashin farashin baƙin mai da canji suke kawo masa naƙasu a kasuwancinsa.

Shugaban ya ƙara da cewa, tashin farashin baƙin man yana da alaka da yadda ake gudanar da mulkin ƙasar nan ba yadda ya kamata ba. A cewar tsohon shugaban, tashin farashin yana jawo cikas sosai a kasuwancinsa na kifi.

Mista Obasanjo wanda ya mallaki sashen kiwon kifi a gidansa dake Abeokuta ta jihar Ogun ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Talatar da ta gabata a yayin taron ƙungiyar daidaita farashi ta makiyayan kifi a Kudu maso yammacin Nijeriya.

Mista Obasanjo ya ƙara da cewa, in dai gwamnati ba ta yi wani abu ba a kan yadda farashin baƙin mai da abincin kifaye yake tashi kullum ba, tabbas makiyayan kifi na Nijeriya za su kasa gudanar da sana’ar a gaba.

Tsohon shugaban ya ba da shawara ga makiyayan kifaye a kan su amince a kan daidaitaccen farashi saboda su cigaba da cin riba a kasuwancinsu. Wanda zai taimaka musu jarinsu ba zai karye ba.

“Farashin baƙin mai yanzu ya kai Naira 800 a kan kowacce lita, farashin kiwata kifi kilo guda ya kama Naira 1400. Ko da ƙaramar riba makiyayan za su ci ba zai yiwu su sayar da kifin a kan farashi ƙasa da Naira 1500. Domin duk wani farashi ƙasa da wannan, faɗuwa ce kai tsaye” Inji shi.

Don haka a cewar sa, manoma sun daina samar da kifi don sayar da shi a farashin tausaya wa masu saye waɗanda kawai su dai a sayar musu da arha ba sa tunanin yadda tasirin tattalin arzikin ƙasar nan yake kawo tazgaro wajen yin harkar kifin ba. Kuma a cewar sa, farashin yana ta ƙaruwa ne saboda masu mulki ba sa yin abinda ya dace a ƙasar nan.

A cewar sa, ko da jarin makiyayan nan na Nijeriya sun karye, to dole dai sai an cigaba da cin kifi a Nijeriya.

Ƙarshe ma dai a dinga shigo da shi daga ƙasashen ƙetare. Don haka, yake kira ga dukkan masu sana’ar harkar kifin su dunƙule guri guda domin ceto sana’ar a Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar masu harkar kofin, Amoo Tunbosun, ya bayyana cewa, a halin yanzu ‘yan Nijeriya suna cinye tan miliyan 3.6 na kifi kowacce shekara. Amma har yanzu ƙasar tan miliyan 1.1 take iya samarwa. To shi ma wannan yana neman gagara a yanzu. Don haka shi ma ya yi kira ga takwarorinsa da su haɗa hannu domin ceto wannan sana’ar.

Wato a cewar sa, su dinga saye da kifin bisa la’akari da kuɗaɗen da suka kashe wajen samar da su. Ba wai farashin tausaya wa masu saye ba, wanda a ƙarshe su ma jarinsu ya zo ya karye.