Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI
’Yan uwa masu karatu, assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, mai ilmintarwa da qayatarwa na Jikin Ɗan Adam, wanda ke kawo muku bayanai game da duniyar jikin bil’adama, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ke aiki a jaridarku ta Blueprint Manhaja mai farin jini.
Barkanmu da wannan lokaci na azumin watan Ramadan; fatan Allah ya karɓi ibadunmu, Aameen. Azumi ya kawo gangara; babu mamaki wannan ne rubutuna na ƙarshe game da tasirin azumi a jikin ɗan adam, sai kuma idan Mai kowa Mai komai ya nuna mana wata shekarar.
Satin da ya wuce, ko ince sati biyu zuwa uku da su ka gabata, na ɗau tsawon lokaci ina bayanin yadda azumi ke da tasirin ga ƙwaƙwalwar ɗan Adam, da kuma zuciyarsa tare da hanyoyin jinin da su ke ɗamfare da ita. Ina fata dai kun fahimci bayanai na.
Rubutun yau cikin Yardar Sarkin halitta, za mu yi duba izuwa tasirin azumi ga sauran gaɓɓai na ɗan Adam, da ma dukkan jiki baki ɗaya; saga nan kuma sai mu ƙarƙare. Tabbas azumin watan Ramadan na da ɗumbin alfanu ga jikin ɗan Adam. Saboda haka ni iya waɗanda na sani zan iya kawo muku kawai.
Shin ko kunsan cewa duk abinda ɗan adam ya ci ko ya sha, guba ne a gareshi? Allah ya yi jikin ɗan adam cikin tsantsar kulawa da kuma matuƙar tsafta ta yadda ba ya son shigar wani baƙon abu cikinsa har sai da dalili ƙwaƙƙwara. Misali, a yayin cin abinci, sinadaran da ake zubawa abincin yayin da yake balaguro daga baki izuwa kayan ciki shi ke sa abincin ya tashi daga ‘guba’, ya zama amfananne ga jikinn ɗan. Haka ma idan maniyyin namiji ya shiga mahaifar mace, a ɗabi’ar jikin ɗan adam shima maniyyin guba ne domin kuwa ‘baƙo’ ne. To amma cikin hikima ta Sarkin halitta, sai a zubo wasu sinadarai da za su lallashi ita mahaifar domin ta karɓi baƙoncin wannan ruwan maniyyi.
To saboda haka idan muka ci abinci, jikin mutum yana ƙoƙari tsayin daka wajen tacewa da zuƙe amfanin abincin, sannan ya bar dusar ta fito waje. Aikin da jiki ke yi kafin ya markaɗa, ya narka, sannan ya tace kuma ya zuƙe amfanin da ke cikin abinci abu ne mai matuƙar buƙatar makamashi mai bayar da kuzari wato “energy” a turance.
Saboda nauyin aikin narkar da abinci a cikin ɗan adam, da kuma yawan makamashin da ƙwayoyin halittun da ke buƙata wajen narka abincin, wasu masanan sun ce aikin narkar da abinci kan iya kawo sanɗa ko nawaa wajen warkewar ciwo, ingantuwar ƙwayoyin halitta da ingantuwar jiki baki ɗaya!
A yayin azumi, wannan aiki (na narka abinci) ba ya wakana a cikin wuni, sai dai bayan anyi sahur da kuma bayan buɗe-baki. Kenan a cikin wunin, ƙwayoyin halittar da Allah ya ɗora wa alhakin narka abinci da zuƙe shi a cikin hutu suke. Hakan zai iya ƙara musu lafiya da ƙarko ya kuma sa su jima su na aiki. Shi yasa a can wani bincike da akayi aka fidda sakamako cewa azumi na hana saukowar tsufa da wuri. Masu yin azumi na nafila ko da bayan Ramadan ne, za su ci moriyar wannan tagomashin!
Haka shi ma yawan saduwa da iyali ya na kawo raunin jiki. Jikin ɗan dam ya na qona makamashin kuzari na ATP da yawa a lokacin da ɗan Adam ke biyan buƙatarsa. To tunda idan ana azumi ba a cin abinci, ba a sha, ba a saduwa, kuma babu wata hanya da jikin zai bi ya shigo da makamashin da zai bashi kuzari, dole jikin ya koyi alkinta ɗan abin da ya ke da shi, tare da amfani da shi ta yadda ya dace. Wannan shi ke sa ayyukan da ke jawo wa jiki tsufa da wuri su kau, sai jiki yayi lafiya da kuzari. Yin azumi kan bawa jikin ɗan Adam damar gudanar da ayyuka irin waɗanda na faɗa a baya: iganta lafiyar ƙwayoyin halittu da jiki baki ɗaya.
Yin azumi ya na bawa jikin ɗan Adam damar yaƙar sinadaran da ƙwayoyin cuta ke fesowa a jiki, waɗanda a turance a ke kira da “togzins”. Lokacin da baki yake a buɗe, ana lalata waɗannan abubuwa masu cutarwa ta hanyar zubo da ruwan da ke narka abinci. Babbar cibiyar da ke tabbatar da cewa an tace jini an tsabtace ga barin irin waɗancan abubuwan “togzins” masu cutarwa ita ce Hanta. Amma idan ana azumi, wasu halittu a cikin jiki da a ke Kira Enzymes su me ke da alhakin gudanar da wannan aikin na lalata togzins da kiyaye jiki daga illarsu.
Kowa ya san idan ana azumi, ana ‘ramewa’ saboda jikinka ko jikinki yana ta ƙone kitsen da aka taskance cikin ma’adanan jiki. A nan, zan ɗan yi waiwaye akan alaƙar abinci da jikin ɗan adam. A lokacin da baki ke buɗe, mukan ci abinci kimanin sau 3 kowacce rana; duk da cewa wasu daga cikin al’umma ba sa samun wannan damar ta yin kalaci sau 3 a rana. Mukanyi karin kumallo, muci na rana, sannan muci na dare. Amma yanzu sai dai mu ci sau biyu- lokacin sahur, da kuma lokacin buɗe-baki.
To, shin yaya jikinmu yakeyi, waɗanne matakai yake bi na cike gurbin abincin rana da ba ma ci lokacin azumi? Yaya jiki yake yi wajen jure wannan doguwar tazara tsakanin abicin sahur izuwa abincin buɗe-baki? Ku biyo ni sannu a hankali domin gano amsoshin waɗannan tambayoyi.
Shi azumi tasirinsa yana da yawa kamar yadda na ce; kayan cikinmu irinsu hanji da tumbi, masu ‘masaukin’ abinci kenan, ba su kaɗai ne ayyukansu ke sauyawa ba lokacin azumi. Gaɓɓai masu ayyukan na musamman irin su ƙoda, hanta, da ƙwaƙwalwa su ma suna sauya salon tafiyar da al’ amura. Dama Malam Bahaushe yana cewa: “idan kiɗa ya sauya, to rawa ma za ta sauya”.
Me yasa mu ke cin abinci ne? Abinci wani jigo ne na gudanar rayuwa, shi muke ci domin mu samu kuzari, mu taskance wani daga ciki, mu gina ƙwayoyin halittu sabbabi domin su maye gurbin tsofaffi, mu gabatar da ayyuka kala kala manya da ƙanana.
Duk lokacin da ɗan adam yaci abinci, masauki na farko da abincin yake tsintar kansa shi ne baki. Bayan haƙora sun taune shi daga nan abincin zai wuce izuwa jannai, wato bututun abinci wanda ya fara daga wuya izuwa tumbi. A tumbi akwai sinadarai iri-iri da za su cigaba da narka abincin har ya shiga ƙaramin hanji, daga nan kuma a zuƙe amfanin abincin a zuba shi cikin jinin da ke zagayawa jiki. Dusar da ba a zuƙe ba kuwa sai ta wuce izuwa babban hanji ko uwar haji inda ake mayar da ita bayan gida.
Wancan amfanin da aka zuƙe aka sanya shi cikin jinin da ke zagayawa, yana bin tsare tsare da yawa saboda ba duka ne za ayi amfani da shi nan take ba. Sannan kuma irin amfanin da za a yi dashi, misali sarrafa ruwan maɗaciya, ko gina katangun ƙwayoyin halittu, ko sarrafa sinadaran “hormone”, da sauransu.
Kash, anan na ke tunanin rufe wannan rubutu game da tasirin azumi a jikin ɗan Adam. Ina fatan Allah ya karɓi ibadunmu, ya sa muna daga cikin ‘yantattun bayinsa, Amin. Allah ya sa a yi bikin sallah lafiya a gama lafiya.
Kafin nan na ke cewa ,‘yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da Yardar Sarkin halitta, domin ci gaba da kawo muku bayani akan jikin ɗan adam. Bissalam. Ayi sallah lafiya.