Tasirin azumi a jikin ɗan adam

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAH

‘Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ilmintarwa, da ke kawo muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ke aiki. 

Barkanmu da wannan lokaci na azumin watan Ramadan; fatan Allah ya karɓi ibadunmu, Aameen. 

Kusan duk lokacin da watan azumin Ramadan ya kewayo, ina sadaukar da rubutuna na wannan watan ga bayanai na yadda azumi ke taka rawa a jikin ɗan Adam. To, wannan shekarar ma, Allah ya sake kawo mu! Sai ku gyara zama domin jin daɗin karatun. Barkanmu !

Azumi ibada ne, kamar yadda kowannenmu ya sani. Malamai su na ta jawabi kan falalolinsa da muhimmancinsa. A wannan rubutu, ni a nawa ɓangaren na lafiya, zanyi iya ƙoƙari na wajen fayyace muku abubuwan da ke faruwa a jikin mai azumi, da yadda hakan ke tasiri a jikin shi ko ita mai azumin. 

Jikin ɗan adam gamayya ne na ƙwayoyin halittu kala kala da su ke da ayyuka mabanbanta. Idan dai ana biye da rubutuna, a baya can, na faɗa cewa jikin ɗan Adam ya ginu ne sakamakon haɗakar ƙwayoyin halittu kimanin guda tiriliyan 100! Sannan kuma akwai ire-iren ƙwayoyin halittu kimanin iri 300, duk a jikin mutum ɗaya! Iko sai Rabbani! 

A duk lokacin da mutum ya yi azumi, to yanayin ayyukan waɗannan qwayoyin halittu na sauyawa matuƙa. Ana samun sauyi wajen buƙatunsu, tattalinsu, ingancinsu, da kuma lafiyarsu. Misali: yin azumi na sanya ƙwayoyin halittu na jiki su rasa ruwan jiki, wanda hakan zai iya haifar da abin da ake kira “dehydration” wato ƙarancin ruwa a jiki. Wannan shi ke sa mutum ya buqaci ruwa sosai bayan anyi buɗe-baki. Batun lafiyarsu kuwa, idan muka ɗauki ƙwayoyin halittu da suka gina sashen da ke narkar da abinci wato “gastrointestinal system”, su na ƙara lafiya da ingantuwar aiki idan mutum ya na azumi. Dalili shi ne lokacin da mai azumi ya ji yunwa, da zarar cikinsa yayi wuni saboda yunwa, akwai wani tururi wanda zubinsa kamar na igiyar ruwa yake; yana tafe yana share duk wani dattin ciki, da ƙananun ƙwayoyin cuta da suke maƙalewa a lungu da saƙo na kayan ciki. 

Shi azumi tasirinsa yana da yawa; kayan cikinmu irinsu hanji da tumbi, masu ‘masaukin’ abinci kenan, ba su kaɗai ne ayyukansu ke sauyawa ba lokacin azumi. Gavvai masu ayyuka na musamman irin su ƙoda, hanta, zuciya, da ƙwaƙwalwa su ma suna sauya salon tafiyar da al’ amura, saboda rashin shigar abinci da abin sha na tsawon lokaci. Dama Malam Bahaushe yana cewa: “idan kiɗa ya sauya, to rawa ma za ta sauya”. Da yardar Allah zan kawo bayanai game da waɗannan gaɓɓai na musamman da yadda su ke tasirantuwa da azumi. 

Ɗan Adam ya na da jiki da kuma ruhi. Azumi na yin tasiri akan jiki da ruhin ɗan Adam gaba daya! Azumi na taimakawa mutum matuƙa wajen koya masa tarbiyyar kai, abin da a turance ake kira da “self discipline”. Tunda mun taɓa wannan fagge, bara mu kawo yadda wani sashen ƙwaƙwalwa ke aiki yayin da mutum ke azumi. Mun san cewa dai ƙwaƙwalwa ke da alhakin tunani, fahimta, yanke hukunci da sauransu.

A ƙwaƙwalwar ɗan adam, akwai wata cibiya da ake Kira ACC (Anterior Cingulate Cortex). Idan mutum na azumi to ita ce ke sa ya bar sha’war zuciyarsa cikin ikon Allah. Wannan cibiya ta na da sauran ayyuka irin su tsayar da zaɓi, tarbiyyar kai da makamantansu.  

Wassafa bigiren wannan cibiya ya na da wahala. Amma idan za ku iya yin hasashe to zan faɗa muku. Idan da za a ce ka zura allura daidai tsakiyar goshin mutum, sannnan ka zura wata daga daidai saitin kunne mutum izuwa cikin ƙwaƙwalwa, to inda alluran su ka hadu, nan ne bigiren wannan cibiya ta ACC. 

Addini ya faɗa mana cewa daga cikin darusssan azumi shi ne ya koya mana la’akari da yadda wasu bayin Allah ke kasancewa cikin halin yunwa saboda rashin abinci. Sai gashi wani bincike na masana ya nuna cewa, wannan cibiya ta ACC ita ce ke da alhakin tarbiyyar kai, tausaya wasu, da kuma yanke hukunci. An wallafa rubutun ne a shafin su na npr.org da ke yanar gizo.

A tsarin aikin jikin ɗan adam , duk abinda a ka yawaita amfani da shi, to haƙiƙa ya kan ƙara girma da ƙarfi, da gwanancewa wajen gudanar da aiki, kamar dai yadda hakan ya ke a rayuwarmu ta zahiri. Saboda haka idan mutum ya na azumi, kuma ya na bin dokokinsa yadda ya kamata, wannan cibiya ta ACC da ke cikin kansa ko kanta za ta ƙara girma da ƙarfi, wanda hakan zai bayu izuwa yawan tausayawa mabuƙata, da tarbiyyar kai wajen ɗa’a ga Allah. 

Har yanzu dai ina kan bayani akan tasirin da azumi ya ke da shi a ƙwaƙwalwa. Ko kun tava tunanin yaya ƙwaƙwalwa ke gudanar da ayyukanta lokacin da ɗan Adam ya ke azumi? Nikam ina yawan tambayar kaina, kuma a matsayina na ɗalibin lafiya ina bincikawa domin gano bakin zaren. Ɗaya daga cikin abinda na fahimta game da kaina shi ne na fi samun fikira da dabarar rubutu a lokacin azumi fiye da a sauran lokuta. 

Mark Mattson farfesa ne na Kimiyyar ƙwaƙwalwa a mashahuriyar makarantar nan wato John’s Hopkins School of Medicine. Ƙwararren masani ne wanda ya nazarci alaƙar azumi da ƙwaƙwalwar ɗan Adam. A yayin tattaunawa dashi, yayi wani furuci wanda ya dunƙule bayanin da nake ta so na baku a wannan gaɓa. Ya ce:” ƙwaƙwalen mutane dole su kasance masu kaifi a yayin rashin abinci. Idan ba haka ba kuwa, to za su gaza samun nasara a yayin ƙoton abinci” 

Wataƙila farfesa ya na nufin mutanen asali waɗanda suka zo a zamanin farko a lokacinda dole ɗan Adam ya fita yayi ƙoto, idan ba haka ba kuwa yunwa ta kashe shi. Farfesa ya ƙara da cewa:” dole waɗannan mutane su zama a wartsake, ya zamto su na aiki da fikirarsu sosai saboda su gano yadda za su yi su samu abinci.”

Wani nature ya ce azumi na sauya yadda ƙwaƙwalwarsa ke aiki. Ya ce:” Na fi yin ayyuka yadda ya dace a lokacin da nake azumi. Na fi jin kuzari, kuma nafi samun damar tafiyar da ayyuka masu tsauri cikin sauki da kwanciyar hankali.”

Wani kuwa cewa yayi: “ Kwanyata ta fi sauri a lokacin da nake azumi. Na fi jin sauƙin yanke shawarar abinda zanyi, kuma na fi jajircewa.” 

A mafi yawan lokuta, idan malaman Kimiyya za su gudanar da bincike, to su na yi ne da ƙananan dabbobi, saboda a wasu lokutan, dabbar sai ta rasa ranta kafin a cimma gaci. Masana kimiyya su kanyi amfani da dabbobi kamar ɓerayen daji, zomaye, da sauransu. A gwaje-gwajen da su ka yi don gano tasirin azumi ga ƙwaƙwalwa, sun shaida cewa azumi ya na daƙile saukowar tsufa da wuri! Sannan ya na rage haɗarin aukuwar ciwuka na ƙwaƙwalwa waɗanda ke da alaƙa da taɓarɓarewar halittun ƙwaƙwalwa. 

‘Yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da Yardar Sarkin halitta, domin ci gaba da kawo muku bayani akan jikin ɗan adam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *