Tasirin azumi a jikin ɗan’adam (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

‘Yan uwa masu karatu, assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka da ilmintarwa da ya ke kawo mu ku bayanai game da duniyar jikin xan adam, wato Jikin Dan Adam, a jaridarku ta Bueprint Manhaja, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, ku san yadda jikinku ya ke yin aiki. 

Barkan mu da wannan lokaci na azumin watan Ramadan tare da fatan Allah ya karvi ibadunmu. Amin. 

A makon da ya gabata, na fara kawo muku bayanin yadda tasirin azumi ya ke a jikin xan adam. Duk da cewa azumi na da tasiri ga ilahirin jiki bai xaya, na zavi na kawo yadda tasirin azumin yake a wasu gavvai na musamman a jikin xan adam. Gavvan su ne: zuciya, qwaqwalwa, qoda, da kuma kayan ciki” Alabasshi daga bisani na kawo tasirinsa ga duk jikin.

A cikin waxannan muhimman gavvai, na xauki qwaqwalwa na fara da ita a cikin rubutun wancan satin. Na faxa cewa yin azumi ya na ‘kunna’ wata cibiya a qwaqwalwa ta sa xan adam ya dinga tunawa da yadda wasu bayin Allah ke ji idan suna hali na yunwa saboda rashin abinci. Haka kuma dai ita cibiyar idan tana aiki, tana koyawa xan adam tarbiyyar kai wajen nisantar sha’awa da soye-soyen zuciya. 

A cikin bayanina na makon jiya, akan tasirin da azumi ya ke da shi a qwaqwalwa, na tambayeku ko kun tava tunanin yaya qwaqwalwa ke gudanar da ayyukanta lokacin da xan Adam ya ke azumi? Nima na kan tambayi hakan. Xaya daga cikin abinda na fahimta game da kaina shi ne na fi samun fikira da dabarar rubutu a lokacin azumi fiye da a sauran lokuta. Kaifa? Kefa?

Na kawo batun Mark Mattson, wanda farfesa ne na kimiyyar qwaqwalwa a mashahuriyar makarantar nan wato John’s Hopkins School of Medicine. Qwararren masani ne wanda ya nazarci alaqar azumi da qwaqwalwar xan Adam. A yayin tattaunawa dashi,  yayi wani furuci wanda ya dunqule bayanin da nake ta so na baku a wannan gava. Ya ce:” qwaqwalen mutane dole su kasance masu kaifi a yayin rashin abinci. Idan ba haka ba kuwa, to za su gaza samun nasara a yayin qoton abinci” 

Bugu da qari, hujjoji da dama da aka samu sanadiyyar binciken Kimiyya yan nuna game da tasirin da azumi ke da shi ga qwaqwalwam an gano cewa: 

  1. Azumi ya na qara dattaku da juriyar qwayoyin halittun qwaqwalwa ta inda idan cutukan qwaqwalwa suka afkawa wannan mutum, to haqiqa abin ya kan zo sauqi. Misalin irin waxannan cututtuka su ne: Alzheimer’s disease, Parkinson’s disease da kuma yawan damuwa. 
    Azumi ya na qara qarfafa ‘igiyoyin musayar saqonni’ (neuronal cell networks) tsakanin qwayoyin halittu na qwaqwalwa. Kafin muyi gaba, zan xan yi fashin baqi.

Ita qwaqwalwar mutum ta na da nata kevantattun qwayoyin halittar da ake kira “neurons”. Akwai su biliyoyi a cikin qwaqwalwar kowanne xan Adam. Kuma suna ‘magana’ da junansu; wato su na musayar saqonni ta hanyar wata tasha da ake kira “synapse” wadda ta ke a tsakanin kowanne neuron xaya da maqwabcinsa. Misali, qwayar halittar qwaqwalwa (neuron) guda xaya a goshi za ta iya magana da takwararta da ke tsakiyar kai da kuma wata da ke saitin kunne ta hanyar abinda ake kira “neural networks” ko hanyoyin sadarwa na qwaqwalwa. Waxannan qwayoyin da suka haxu su ke musayar saqonni a tsakaninsu suna qara qarfin alaqa a duk lokacin da wani abu da zai sa su yi aiki ya afku. Gwargwadon maimatuwar aikin, gwargwadon qaruwar qarfin alaqar da ke tsakaninsu! Wannan shi ne ke sa mutum ya gane iyayensa; ya kuma haddace karatunsa, matuqar ya na yawan nanatawa. 

Idan ba a manta ba, a satin da ya wuce, na yanko maganganun da farfesa yayi akan azumi. Shi wannan farfesa ya gudanar da zuzzurfan bincikensa ne akan tasirin da azumi ya ke yi ga qwaqwalwar xan Adam. To a wannan gavar ma, ina so na kawo abinda farfesa Mattson ya ce :” wani abinda muka gano kwanan nan shi ne azumi zai iya rage yawan damuwa, ya kuma kare faruwar cutukan qwaqwalwa ta hanyar qarawa igiyoyin sadarwa tallafi ta yadda za su kula da yanayin sadarwar da ke faruwa tsakaninsu”

Sama da shekaru dubu biyu da su ka shuxe, an yi amfani da yin azumi don neman waraka da ciwon Farfaxiya. Kuma har yanzu ana amfani da wannan dabara. To kenan idan mutum ba shi da ciwon farfaxiya, azumi zai iya rage haxarin afkuwar wannan ciwo a rayuwar xan Adam kenan. 

  1. Azumi ya na inganta walwalar mutum. Na kawo misalai daga bakin wasu ma su azumi da aka tambaye su yadda suke ji idan su na azumi. 

Wani nature ya ce :”azumi ya na sauya yadda qwaqwalwata ke aiki”,  sannan ya qara da cewa :” Na fi yin ayyuka yadda ya dace a lokacin da nake azumi. Na fi jin kuzari, kuma nafi samun damar tafiyar da ayyuka masu tsauri cikin sauki da kwanciyar hankali”.  Wani kuwa cewa yayi: “ Kwanyata ta fi sauri a lokacin da nake azumi. Na fi jin sauqin yanke shawarar abinda zanyi, kuma na fi jajircewa.” 

Azumi ya na inganta kevantattun ayyukan qwaqwalwa, wato ayyukan qwaqwalwa na musamman irinsu lura, nutsuwa, hankali, nazari, la’akari, bacci, yanke shawara, fikira, da sauransu.  A cewar Dr. Philips, “rahotanni sun nuna cewa lafiyayyun mutane ma su azumi su na samun qaruwar fahimta, kuzari, bacci mai daxi, walwala, da mutunta-kai”        

A bitar wani bincike da a ka yi akan mutane masu yin azumin watan Ramadan, a ciki an samu wani nazari da akayi da mutane Goma sha uku. An gwada yanayin baccinsu bayan sunyi sati guda suna azumi. Sakamakon ya nuna cewa an samu qarin armashi cikin baccinsu, lurarsu, da kuma yadda su ke ji a duniyar zamantakewarsu da jama’a. Saboda haka lallai azumi ya na daidaita Ruhin xan Adam da kuma jikinsa, ya saita shi bisa hanya. Azumi ya na tsarkakejiki, ya kuma yi wa imaninmu chaji! 

‘Yan uwa, ku tara a mako mai zuwa da Yardar Sarkin halitta, domin ci gaba da kawo muku bayani akan jikin xan adam.

Mustapha Ibrahim Abdullahi
Lamba: 08037183735
Email: [email protected] gmail.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *