Tattalin arzikin ƙanƙara ya samu cigaba yayin bikin bazara na Ƙasar Sin

Daga CRI HAUSA

Yayin da ake murnar bikin bazara na shekarar Damisa na gargajiyar ƙasar Sin, kayayyakin masu alamar musamman na wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing, da ake kira Bingdundun sun fi na Damisa samun karɓuwa, har ma samun su na da matuƙar wahala.

Ana iya cewa, kasuwar sayayya ta hutun bikin bazara na ƙasar Sin ta ƙara haɓaka yayin da ake kallon wasannin Olympics na lokacin sanyi, tattalin arzikin ɓangaren wasannin ƙanƙara yana ingiza ci gaban tattalin arzikin ƙasar ta Sin.

A shekarar 2015, lokacin da Sin ta gabatar da roƙon shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi, an yi alƙawari cewa, za a yi ƙoƙari domin al’ummun Sinawa miliyan 300 su halarci wasan ƙanƙara, kuma zuwa yanzu, an riga an cimma wannan burin.

Ya zuwa watan Oktoban bara wato shekarar 2021, adadin Sinawa waɗanda suka halarci wasan ƙanƙara ya kai miliyan 346, adadin da ya kai kaso 24.56 bisa ɗari na ɗaukacin al’ummun ƙasar Sin.

Daga wasan ƙanƙara, da yawon shaƙatawa dake shafar ƙanƙara, da sana’o’in samar da kayayyakin wasan ƙanƙara, da kuma hada-hadar kuɗi dake shafar sana’o’in ƙanƙara, an lura cewa sana’o’in ɓangaren ƙanƙara na ƙasar Sin sun samu ci gaba daga dukkan fannoni.

A halin yanzu, duk da cewa, annobar cutar COVID-19 tana ci gaba da bazuwa a sauran sassan duniya, kasuwar sayayya ta ƙasar Sin tana ƙara haɓaka. Dalili shi ne, a ko da yaushe gwamnatin ƙasar Sin tana sanya lafiyar al’ummunta a gaba da komai, kana tana ɗaukar matakan da suka dace yayin kandagarkin annobar da ƙoƙarin ingiza ci gaban tattalin arzikin ƙasar, waɗanda suka nuna cewa, kamfanonin ƙasa da ƙasa su ma suna iya cin gajiya daga “damarmakin ƙasar Sin” sakamakon ƙaruwar buƙatun babbar kasuwar ƙasar.