Tattalin arzikin ƙasar Sin yana taimakawa farfaɗowar tattalin arzikin duniya

CRI HAUSA

Yau Asabar ne aka ƙaddamar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar ƙasar Sin, inda rahoton ayyukan gwamnatin da aka gabatar don a dudduba shi ya yi nuni da cewa, dole ne a ƙara sa muhimmanci kan samun ci gaba ba tare da tangarɗa ba.

Shekarar 2021 tana da muhimmiyar ma’ana ga ƙasar Sin. Duk da barazana da ƙalubaloli daban-daban da ta fuskanta, ƙasar Sin ta ci gaba da farfaɗo da tattalin arzikinta. Ta cimma manyan manufofinta yadda ya kamata. Jimillar tattalin arzikin ƙasar Sin a bara ya kai dalar Amurka triliyan 3, wanda ba a taba ganin irinsa a tarihin duniya ba.

Aiki ne mai wahala da ƙasar Sin ta kai ga cimma kyawawan sakamako. Hakan ya nuna cewa, ƙasar Sin na da ƙarfin juriya wajen raya tattalin arziki, tana daidaita barazana yadda ya kamata, kana kuma hakan na da nasaba da yadda take yaƙi da annobar COVID-19, da kuma sa muhimmanci kan samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar ƙasa ba tare da tangarɗa ba.

Ƙasar Sin ta sanya burin daga yawan GDPn ƙasar da kaso 5.5 bisa dari a shekarar 2022. Ta yi tunani sosai kan halin da take ciki a gida da waje ta fuskar bunƙasa tattalin arziki, kana adadin ya dace da haƙiƙanin yanayin bunƙasar tattalin arziki. Ya cancanci yadda ƙasar Sin take raya tattalin arziki ba tare da tangarɗa ba.

Da zummar cimma burinta, a bana ƙasar Sin za ta ci gaba da buɗe ƙofa ga waje, za ta duba yiwuwar nazarin ɓangarorin da ƙasashen waje ba za su iya zuba jari ba, domin tabbatar da an ba su damarmaki kamar takwarorinsu na cikin gida, za ta kuma ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci, a ƙoƙarin shigar da karin jarin waje. Buɗaɗɗiyar kasuwar ƙasar Sin za ta shigar mata ƙarin jarin waje, kana kuma za ta samar wa kamfanonin ƙasa da ƙasa damarmaki na samun ci gaba a ƙasar ta Sin.

Fassarawa: Tasallah Yuan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *