Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Arzikin Nijeriya ya ƙaru a tsakanin watan Yuli da kuma Satumba da kashi 3.46 cikin ɗari kamar yadda alƙamun hukumar ƙididdiga ta ƙasar, NBS, da aka fitar ranar Litinin suka nuna.
Alƙaluman sun nuna yadda arzikin cikin gida na ƙasar ya bunƙasa a rubu’i na uku na gwamnatin Bola Tinubu.
Tattalin arzikin cikin gida (GDP) na nufin dukkanin harkokin tattalin arziki na kamfanoni da gwamnati da ɗaiɗaikun jama’a na cikin ƙasa.
To, Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya, NBS, tana wallafa alƙaluman da ta samu bayan ta tattara bayanai kan waɗannan harkokin tattalin arziƙi a cikin wata uku-uku a shekara, ta fitar da sakamakon da alƙaluman suka nuna mata da abin da suke nufi.
Da wannan ne hukumar ta NBS ta fitar da bayanin cewa arziƙin Nijeriyar ya bunƙasa a wannan lokaci da ta bayyana.
Kamar dai yadda hukumar ta NBS ta ce arzikin cikin gida na Nijeriyar ya ƙaru a rubu’i na uku na wannan shekara ta 2024, wannan na nufin arziƙin ya zarta wanda aka samu a rubu’i na uku na bara, wanda a lokacin aka samu kashi 2.54 cikin ɗari ya kuma wuce wanda aka samu na rubu’i na biyu a wannan shekara ta 2024 inda aka samu 3.19.
Bayanan hukumar sun nuna cewa ɓangaren bankuna da harkokin sadarwa da fasaha da ayyukan lauyoyi da makamantansu ne suka fi haifar da ƙarin da aka samu – inda suka bunƙasa da kashi 5.19, wanda hakan ya tallafa wa arziƙin ƙasar ta wannan bunƙasa da ya yi da kashi 53.58 cikin ɗari.
To, shi dai arziƙin cikin gida na Nijeriyar ya kai na naira tiriliyan 20.12, wato ke nan ya ƙaru daga Naira tiriliyan 18.29 a rubu’i na biyu na wannan shekara ta 2024, ya kuma ƙaru daga Naira tiriliyan 19.44 a rubu’i na uku na 2023.
ƙididdiga ta nuna cewa arziƙin na cikin gida ya kai naira tiriliyan71.13 a don haka wannan ya nuna an samu ƙaruwarsa da kashi 17.26 shekara bayan shekara.
ɓangaren harkokin noma ya bayar da kashi 26.51 cikin ɗari, sai kasuwanci ya samar da kashi 14.78 cikin ɗari da sadarwa, kashi 13.94 cikin ɗari, sai ɗanyen mai wanda ya bayar da kashi 5.57 cikin ɗari da kuma ɓangaren gidaje wanda ya bayar da kashi 5.43 cikin ɗari ta bunƙasar.
A ɓangaren manyan harkokin ayyukan noma sun bunƙasa da kashi 1.14 cikin ɗari, sai masana’antu da ya ƙaru da 2.18 cikin ɗari, sai harkokin bankuna da makamantansu waɗanda suka ƙaru da kashi 53.58 cikin ɗari, inda wannan ɓangare ke nan shi ya fi bunƙasa shekara bayan shekara.
ɓangaren man fetur ya bunƙasa ne da kashi 5.17 inda ya bayar da kashi 5.57 ga bunƙasar arziƙin na cikin gida – kasancewar ƙasar na haƙar mai ganga miliyan 1.47 a kullum.
Shi kuwa ɓangaren da ba na mai ba ya bayar da gudunmawar kashi 94.43, kuma harkokin noma da kasuwanci da sadarwa (waya da intanet da sauransu) da harkokin gidaje ne suka haifar da wannan bunƙasa.
Yawancin masana tattalin arziƙi da ‘yansiyasa da masana harkokin kasuwanci suna son ganin bunƙasar arzikin cikin gida.
A wajensu idan aka samu wannan bunƙasa, hakan na nufin kuɗin da mutane ke kashewa ya ƙaru, ana hada-hada sosai ke nan.
Idan kuma arziƙin na cikin gida ya yi ƙasa hakan na nuna cewa al’ummar ƙasa ba sa jin daɗi, harkokin kasuwanci ba sa gudana, ma’aikata da yawancin jama’a na cikin mawuyacin hali.
Idan alƙaluman arzikin suka yi ƙasa a rubu’i biyu na shekara a jere to wannan ake cewa tattalin arziƙin ƙasa ya kama hanyar durƙushewa – wannan ne zai kai ga rasa aiki ko rage ma’aikata da sauran matsaloli na tattalin arziki