Tattaunawa ce kaɗai mafita tsakanin Rasha da Ukraine – Chana

Shugaban Ƙasar Chana Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky ta wayar tarho, kamar yadda fadar gwamnatocin ƙasashen biyu suka tabbatar, wanda shi ne kira na farko da shugabannin biyu suka yi tun bayan kaddamarwa ƙasar da Rasha ta yi.

“Na yi doguwar tattaunawa mai ma’ana ta wayar tarho tare da shugaba Xi Jinping,” inji Zelensky a shafin Twitter. “Na yi imanin cewa, wannan tattaunawa da aka yi, da kuma naɗa jakadan Ukraine a Ƙasar Chana, za su ba da ƙwarin gwiwa wajen raya dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.”

Mai magana da yawun Zelensky Sergiy Nykyforov, ya bayyana a shafin Facebook cewa, shugabannin biyu sun ɗauki kusan sa’a guda suna tattaunawar ta wayar tarho.

Bayan tattaunawar, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya naɗa sabon jakada a birnin Beijing na ƙasar ta Chana.

Pavel Ryabikin, wanda a baya ya jagoranci ma’aikatar masana’antu a ƙasar ta Ukraine, an naɗa shi a matsayin sabon manzon Ukraine a Ƙasar Chana, a cewar sanarwar fadar shugaban ƙasar.

Ukraine dai ba ta da jakada a Chana tun watan Fabrairun shekarar 2021.

Gidan talabijin na CCTV na Ƙasar Chana, ya ba da rahoton cewa, yayin tattaunawa a tsakanin shugabannin biyu, Xi ya shaida wa Zelensky, cewa, tattaunawa ita ce kaɗai mafita a rikicin da ke wakana tsakanin ƙasashen biyu.

Tashar talabijin ta CCTV ta bayar da rahoton Xi Jinping na cewa, Ƙasar Chana na tsayawa tsayin daka kan batun zaman lafiya, kuma babban matsayinta shi ne inganta shawarwarin zaman lafiya a tsakanin ƙasashen biyu.

Ƙasar Chana ta kuma sanar da cewa, za ta aike da tawaga zuwa Ƙasar Ukraine da nufin neman hanyar warware rikicin siyasa a ƙasar.

Ma’aikatar harkokin wajen Ƙasar Chana, ta bayyana a wani taron manema labarai cewa, za a aike da wakilin gwamnatin ƙasar mai kula da harkokin yankin Eurasia, da zai ziyarci ƙasar Ukraine da sauran ƙasashen duniya, domin tattaunawa mai zurfi kan yadda za a warware rikicin ƙasar ta Ukraine, amma a siyasance.