Tawagar jami’an lafiya na ƙasar Sin ta bayar da gudunmuwar kayayyakin lafiya a ƙasar Saliyo

Daga CMG HAUSA

Tawagar jami’an lafiya na ƙasar Sin dake aiki a Saliyo, ta samar da gudunmuwar kayayyakin lafiya ga asibitin sada zumunta na Sin da Saliyo, domin bunƙasa hidimomin kiwon lafiya.

Shugaban tawagar Zhou Xi, ya ce kayyakin sun haɗa da rukunoni 24 na magungunan da ake buƙata sosai da sama da nau’o’i 30 na kayayyakin aiki, waɗanda za su taimaka wajen cike gibin ƙarancin kayayyakin lafiya dake akwai a asibitin.

A cewar Zhou Xi, asibitin, wanda a nan ne tawagar ta ƙasar Sin ke aiki, ya dade yana fuskantar ƙarancin kayayyaki da wutar lantarki da ruwa, wadanda ke zaman barazana ga marasa lafiya da ma ma’aikata.

Ya ce duk da annobar COVID-19 da wasu tarin ƙalubale, daga farkon bana zuwa yanzu, tawagar ta yi nasarar gudanar da tiyata sama da 40, yana mai cewa, jami’an tawagar za su dage wajen musayar dabaru da takwarorinsu na Saliyo da kuma ci gaba da kulawa da marasa lafiya na ƙasar.

Mai Fassara: Fa’iza Mustapha