Daga BELLO A. BABAJI
Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN ya ce yana aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA) don gyara tashar lantarkin Shiroro-Kaduna wanda ya haddasa raguwar wuta a jihohin Kaduna, Kano da ma wasu manyan biranen Arewa.
Cikin wata takarda da Janar-Manaja na hulɗa da jama’a na TCN, Ndidi Mbah ya fitar, ya ce kamfanin na aiki tuƙuru wajen ganin dawo da raba isasshen lantarki duk da ƙalubalen tsaro da yankin ke fuskanta.
Rahotonni sun bayyana cewa, wutar yankin ta samu tsaiko ne sakamakon lalata ta da ƴan ta’adda suka yi wanda saboda haka ne TCN ya haɗe kai da ofishin NSA don shawo kan matsalar.
Mbah ya ce, an samu jinkiri ne wajen gyaran layin Shiroro-Mando wanda shi ke bai wa shiyyar wuta sakamakon ayyukan ta’addanci da ke gudana inda a yanzu haka su na aiki da ƙwararrun injiniyoyi don shawo kan matsalar.