TETFund ta raba bilyan N300 ga manyan makarantu 226

Daga AISHA ASAS

Hukumar Tallafa wa Manyan Makarantu (TETFund) ta ce ya raba kuɗi sama da Naira bilyan 300 a tsakanin manyan makarantu 226 a cikin wannan shekara ta 2021 domin samar da gine-gine da kuma horar da malamai.

Shugabam Kwamitin Amintattu naTETFund, Alhaji Kashim Ibrahim-Imam, shi ne ya bayyana hakan yayin wani taronsu a Asaba, jihar Delta a ranar Litinin.

Ya ce TETFund ta ba da himma wajen bunƙasa fannin ilimi ta hanyar bai wa malamai horo da kuma samar da gine-gine don yauƙaƙa sha’anin koyo da koyarwa.

A cewar Ibrahim-Imam, TETFund ta shekara 10 da kafuwa, kuma sun samu nasarar aiwatar da ayyuka har guda 10,000 cikin waɗannan shekarun a tsakanin manyan makarantun ƙasar nan.

“Nasarorin da muka samu a bayyane suke, mun kammala wasu ayyukan da dama yayin da wasunsu na kan gudana.

“Daga ziyarar da na kai wurare daban-daban, ayyukan da na gani suna gudana duk sun wuce kashi hamsin da kammaluwa.

“Ina tabbatar wa ɗaukacin manyan makarantun ƙasar nan cewa za mu yi aiki fiye da yadda muka yi a baya,” in ji Ibrahim-Imam.

Ya ƙara da cewa, tun bayan kafuwar TETFund shekaru 10 da suka gabata, asusun ta yi nasarar horar da malamai sama da 30,000 daga sassan ƙasar nan a ciki da wajen ƙasa.