Tikitin Musulmi da Musulmi: Yadda Babachir da Yakubu Dogara ke yaƙar Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Saɓani, rashin jituwa da rikici a kan takarar Musulmi da Musulmi ta Bola Tinubu da Kashim Shettima a APC, ta ƙara muni da tayar da ruɗani a cikin APC a makon jiya, yayin da wasu manyan jam’iyyar suka tabbatar cewa sai sun kunyata APC a zaɓen 2023.

Lamarin ya yi tsamarin da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal suka kira taron Manyan Kiristocin Arewa ‘Yan APC, a ranar Juma’a a Abuja, suka yi wannan barazana.

Dama kuma Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), ta yi tofin tsinuwa kan ɗaukar Shettima a matsayin mataimakin takarar shugaban ƙasa na APC, inda ƙungiyar ta ce cin mutunci ne ga ɗaukacin kiristocin Nijeriya.
Yi wa lamarin tir ya qara ƙamari lokacin da aka yi zargin APC ta ɗauki sojojin hayar fasto-fasto na bogi, su ka shiga taron ƙaddamar da Shettima. A nan ma CAN ta yi tir da lamarin.

Kafin Lawal da Dogara su haɗa ƙarfi wuri ɗaya, Babachir Lawal tuni ya fito ya nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya qi amincewa da Shettima, domin a cewarsa, an yi wa Kiristocin Arewa rashin adalci. Sai dai kuma Buhari bai yi hakan ba.

Babachir na daga cikin ‘yan kwamitin da suka bayar da shawarar wanda Tinubu ya kamata ya ɗauka.

Jin haushin ɗaukar Shettima ya sa Babachir ya ƙudiri aniyar tarwatsa ƙudirin APC. “Tuni an ba mu goron gayyata zuwa yaƙi. Har mun isa sansani, mun kafa tantina,” inji Babachir.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawal da tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, sun ƙara fitowa fili sun nuna rashin amincewar kan takarar Bola Tinubu da Kashin Shettima a APC, takarar da ake kira ‘Muslim-Muslim Ticket’, saboda su biyun duk Musulmai ne.

Babachir Lawal ya ce Kiristoci ‘yan APC za su yi amfani da katin zaɓensu domin su koya wa APC hankali, tunda hankalinta ya gushe a jikinta.

Babachir ya ce duk zancen banza ne da ake cewa wai cancanta ce ta sa Tinubu ya ɗauki Kashim Shettima ya yi masa takarar mataimaki, ba addini ba.

Lawal ya ce tsarin ‘Muslim-Muslim’ wata daɗaɗɗiyar ajanda ce ta ture Kiristoci daga mulkin ƙasar nan.

Ya buga misali da ɗaukar Kashim Shettima matsayin mataimakin takarar Tinubu, rashin Kiristoci Kwamitocin NWC da NEC na Jam’iyyar APC, ya ce duk tuggun ture Kiristoci ne.

“Kada ma a kawo mana wani rainin wayau a ce wai babu ruwan addini idan ana maganar siyasa. Domin abin da ke faruwa a APC daɗaɗɗen shiri ne sai yanzu aka samu damar fito da shi.

Saboda haka ya ce tun da wuri bai kamata APC ta ci gaba da tafiyar tikitin Musulmi da Musulmi ba, saboda ba wani abin alherin da zai kawo, sai dai qara rarrabuwar kawuna tsakanin Musulmi da Kirista a Nijeriya.

Shi ma tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara, ya yi fatali, tir da Allah–wadai da abin da APC ta yi, wanda ya ce babban kuskure ne da rainin wayo, a ce duk cikin Kiristocin Arewa babu wanda zai iya zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a APC.

“Tinubu ya yi babban kuskure tunda har ya biye wa gungun waɗanda suka kitsa tuggun raina mana wayo.”

Dogara ya ce Kiristocin APC za su yi amfani da katin zaɓe domin su koya wa APC hankali.
Cikin manyan baqi har da Sanata Elisha Agbo da Solomon Dalung.

“Wannan rainin hankali da aka yi mana, zai zama tayar da mu ne daga barci aka yi wa mu Kiristocin Nijeriya. Ba mu muka fara wannan siyasar addini ba. APC ce da ‘yan takarar ta su ka fara. Don haka kowanen mu ya tashi tsaye ya yi abin da ya dace mu yi.”

Dogara ya ce takarar Musulmi da Musulmi siyasar nuna fifiko ce aka yi wa Kiristocin Nijeriya, kuma an dasa bambanci da rabuwar kawuna kenan.

Bayan taron manyan Kiristoci a Abuja, Dogara da Babachir sun ziyarci Gwamna Samuel Ortom na Benuwai da Nysome Wike na Ribas.

Duk da dai Shugaban APC Abdullahi Adamu da Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje sun ragargaji Babachir da masu sukar Tinubu saboda ya ɗauki Shettima takarar mataimakinsa.

Shi ma Wike da ya karɓi baƙuncin Dogara da Babachir, ya na da jiƙaƙƙa mai tsamari tsakaninsa da Atiku Abubakar, ɗan takarar PDP na zaɓen 2023. Matsalar ta su ta bijiro ne kan fitar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP, inda ta kai har kwana ɗaya kafin ziyarar Dogara da Babachir, sai da Wike ya buɗe wa Atiku wuta, tare da kiran sa tantagaryar maƙaryaci, a wani raddi da ya mayar wa Atiku ɗin.

Saboda haka idan ma Dogara da Babachir na son kamun ƙafar haɗa kai da PDP ne, to Wike ba zai kasance ɗan jagoran da zai kai su ga nasara ba.

Kwanan baya shi ma Wike ɗin an ce ya karɓi baƙuncin gwamnoni uku na jihohin Yarabawa masu kusanci da Tinubu. Wasu na ganin cewa Tinubu ne ya turo su wajen Wike ɗin. Shin ko kuwa Dogara da Babachir sun gargaɗi Wike kada ya haɗa kai da APC ne?

Su ma su Dogara da Babachir har yau ba mu ji sun gana da Gwamnonin APC ba. Shin ko gwamnonin babu ruwan su da sha’anin na su ne, su biyu ke kiɗan su, kuma su ke yin rawar su ne?

APC na da Gwamnoni Kirista 6 cikin 22 da ta ke da su a ƙasar nan. Simon Lalong na Filato ne kaɗai Gwamna Kirista a APC a Arewa, kuma sunansa na cikin sunayen da aka bai wa Tinubu domin ya zavi ɗan takarar mataimaki a cikinsu. An ce an haɗa da sunayen Babachir da na Dogara. Amma sai Tinubu ya ɗauki sunan Shettima, Musulmi kamarsa. Wannan abu ya vata wa Kiristoci rai, musumman ma na Arewa.

Har yau ba a ji Lalong ya caccaki ɗaukar Shettima ɗan takarar mataimaki ba. Sai ma ji aka yi shi ne za a naɗa daraktan kamfen ɗin Tinubu.

Sauran Gwamnonin APC biyar duk a Kudancin Nijeriya su ke. Dukkan su kuma su na yin kalamai ne cikin taka-tsantsan, su na cewa a daina gwamutsa siyasa da addini.