Tinubu ba zai yi nadamar naɗa ni minista ba, inji Wike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Laraba ne tsohon gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike ya yi alƙawarin cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba zai yi nadamar naɗa shi minista ba.

Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana gaban majalisar dattawa domin tantancewa.

Ya taɓa riƙe mukamin minista a zamanin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan.

Da yake tunawa da yawancin ayyukan da ya yi a matsayin gwamna, Wike ya ce: “Waɗannan abubuwan za a iya cimma su idan kun jajirce kuma idan kuna da sha’awar aikin.”

Ya ce tsofaffin gwamnoni da dama suna sha’awar zama minista amma ba su da sha’awar yin hidima.

“Na gode wa Shugaban Ƙasa da ya zave ni. Na yi imani, sanin irin damuwar da shugaban ƙasa ke fama da shi don magance matsalolin Nijeriya, ba mu da wani zavi illa mu ba shi tallafin da ake buƙata.

“Kuma zan iya tabbatar muku, idan aka tabbatar da ni a kowane matsayi, shugaban ƙasa ba zai yi nadamar naɗa ni ba.”

Wike shi ne ɗan takarar Jam’iyyar PDP ɗaya tilo a jerin ministocin Jam’iyyar APC da Shugaban Ƙasa ya aika wa majalisar dattawa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Bayan gabatar da jawabin nasa, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya shaida ƙwarewa da qarfin da Wike ke da shi a ofis sannan ya nemi ya ɗauki baka yayin da majalisar ta wanke shi.

Har ila yau, a ranar Laraba ɗin, jam’iyyar PDP reshen jihar Ribas ta caccaki tsohon ɗan takarar shugaban qasa Atiku Abubakar da magoya bayansa kan ƙoƙarin vata sunan Wike biyo bayan naɗa shi a matsayin minista.

Kakakin ƙungiyar kamfen ɗin PDP na Ribas, Ogbonna Nwuke, ya yi mamakin dalilin da ya sa jaruman da “ɗan takarar shugaban qasa na PDP da ya sha kaye, Atiku, ke jagoranta, suke gudanar da taro kan yadda za a yi da Wike”.

Nwuke ya ce: “Shawarar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yanke na naɗin maza da mata da suka dace, ciki har da tsohon Gwamna Nyesom Wike, don yi wa ƙasa hidima, ‘yan Nijeriya masu son ci gaba ne ke yabawa a matsayin wani gwani a ƙoƙarin qƙato ƙasarsu.

“Ya bayyana cewa waɗanda kawai ba sa son jajircewar yunƙurin ceto da haɗa kan Nijeriya da Shugaba Bola Tinubu ya yi su ne waɗanda ta hanyar martanin da suka yi a lokacin wani babban lamari na gaggawa na ƙasa ba sa yi wa ƙasar fatan alheri.”

Nwuke ya ce ana yaba wa gwamnati mai ci a duniya bisa ƙudurin ta na samar da mafita ta hanyar ɓangarenci.

Ya ce: “A yin haka, gwamnati ta ƙuduri aniyar bari na baya-bayan nan su zama na baya, ta kuma miƙa hannunta ga ‘yan Nijeriya masu ra’ayin siyasa daban-daban domin su haɗa kai da ita wajen ƙwato ƙasarmu gaba ɗaya daga ƙangin koma bayan tattalin arziki, da taɓarɓarewar siyasa da tsaro.

“To mene ne matsalar gungun masu ruɗani a cikin PDP waɗanda saboda son kai suke son a yi yaƙi da Wike, mutanen Nijeriya da gwamnatin Tinubu?”.

Ya lura cewa Wike, “wanda ya yi gwagwarmaya don sake gina PDP kafin zuwan masu haddasa husuma, mutanen Nijeriya nagari, waɗanda suka yi gwagwarmayar tabbatar da adalci da kuma gwamnatin kishin ƙasa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu”, ba za su taɓa yarda da son kai ba, marasa kishin ƙasa don daƙile shirin ceto Nijeriya.

Nweke ya ce: “Sai akasin haka, sun ƙuduri aniyar barin ƙasar Masar tare da duk waɗanda suka yi imani da gina sabuwar Nijeriya; dukkansu suna mutunta ɗiyaucin al’ummar Nijeriya saboda ƙasar da aka alƙawarta.

“Manufar Nijeriya ta fi ta mutum ko gungun mutane girma. Tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida ya sha jaddada wannan batu.

“Babu wani zagon ƙasa, tsoratarwa, tada hankali da barazana da za su hana tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Barista Nyesom Wike amsa kiran aiki a lokacin da ƙasar ke cikin gaggawa.

“Waɗanda ke taruwa kamar ungulu da ke zagayawa a sararin sama, su ne ainihin maƙiya kuma maƙiyan Nijeriya na gaske.

“Su ne waɗanda ke cin riba a lokacin da jama’a ke shan wahala, kuma su ne ke haifar da rashin haɗin kai, rashin zaman lafiya, rashin tsaro da yaɗuwar talauci da bai dace ba.

“Suna zargin Wike da bayyana Jam’iyyar APC a matsayin jam’iyya mai cutar daji. Kamar yadda al’amura ke fama da cutar kansar da APC ke fama da ita har yanzu ba ta koma tavarvarewa ba. Hakan na nufin ciwon daji da ke addabar Jam’iyyar APC ba zai warke ba.

“Ta hanyar taimakon Allah, yanzu Nijeriya ta samu sabon shugaba wanda ta hanyar yi masa tiyatar gyaran jiki ya himmatu wajen warkar da cutar kansa gaba ɗaya.

“Wannan shi ne ginshiƙin injiniyan siyasa da Shugaba Tinubu ya fara.

“Sun jiyo tsohon gwamna Wike yana cewa ba zai zama Minista ba. Bambancin shine Nijeriya ta miƙa hannun zumunci ga duk mai ƙaunarta.

“Nijeriya na jinjinawa kuma duk wani ɗan kishin ƙasa na gaskiya wanda ya yi imani da manufar ƙasar nan mai cike da tarihi dole ya amsa kiran.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *