Tinubu bai buɗe iyakokin Nijeriya ba – Kwastom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Hana Fasa Ƙauri ta Ƙasa (Kwastam) ta ce har yanzu Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bai sake buɗe dukkan iyakokin ƙasar nan da tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta rufe ba.

Idan za a tuna a shekarar 2019 ne, Buhari ya rufe dukkan iyakokin ƙasar nan domin hana shigo da wasu kaya ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda suka haɗa da shinkafa, bindigogi da sauransu.

Bayan shekaru biyu, gwamnatin Buhari ta sake buɗe wasu kaɗan daga cikin iyakokin, wasu kuma sun kasance a rufe duk da kokawar da ‘yan Nijeriya suka yi.

A kwanakin baya ne wasu mutane suka fara yaɗa wani tsohon faifan bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka ga Konturola na hukumar NCS reshen Ogun, Bamidele Makinde ya buɗe shingen da ke kan iyakar Idiroko da Jamhuriyar Benin.

An yaxa bidiyon tare da cewa Tinubu ya sake buɗe iyakokin qasar nan.

Da yake mayar da martani, Konturola na NCS ya ce gwamnatin Tinubu ba ta bada umarnin sake buɗe dukkan iyakokin ƙasar nan ba.

A cewarsa, gwamnatin Buhari a shekarar 2022 ta sake buɗe iyakar Idiroko da wasu ‘yan tsiraru, inda ya ce sauran na ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu qarin umarni daga gwamnatin tarayya.

Bamidele ya bayyana cewa, sauran iyakokin da aka amince da su a jihar Ogun kamar Ijofin, Imeko, Ijoun da kuma Ohunbe na nan a kulle.

“Idiroko ne kawai aka buɗe yanzu; sauran kuma har yanzu a kulle suke,” inji shi.

Makinde, yayin da yake zantawa da manema labarai a Abeokuta, ya ci gaba da cewa jami’an Kwastam ma’aikatan gwamnati ne, waɗanda aikinsu shi ne aiwatar da manufofin gwamnati.

“Yanzu, muna da sabuwar gwamnati. Sabuwar gwamnati za ta zo da manufofinta. Bai kamata a sami kuskure ba. Mu ma’aikatan gwamnati ne kawai, muna aiwatar da manufofi. Duk abin da Abuja ta ce muna yi,” a cewarsa.

Ya jaddada cewa, “Iyakar Idiroko na buɗe ko fa yaushe, amma a sauran idan muka kama mutum za mu ƙwace kayansa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *