Tinubu da Osinbajo: Wa zai kai wani ƙasa a APC?

*Siyasar ‘uba’ da ‘ɗa’ ta kunno kai a cikin jam’iyyar
*Tinubu ya ‘sheganta’ Osinbajo
*Yaro ya yi wa maigidansa ƙirmisisi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A daidai lokacin da manyan zaɓukan 2023 ke ƙara tunkarowa, masu sha’awar taka takarar kujerar shugabancin Nijeriya a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar sai ƙara bayyana kansu suke yi ga al’umma tare da tuntuvar masu ruwa da tsaki, don neman shawarwari da goyon bayansu.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jagoran Jam’iyyar APC na Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbanjo, su ma kamar sauran manema, sun fito sun nuna kwaɗayinsu na gadon kujerar Shugaba Buhari a zaɓen na 2023.

Tuni dai tsohon Sanata Tinubu ya fara bayyana sha’awarsa ta tsaya wa takarar kujerar Shugaban ƙasa a 2023, har ma takararsa ta zama jiki.

An ga wani bidiyo da aka yaɗa ta talabijin da kafofin sada zumunta, Farfesa Yemi Osinbajo yana bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen 2023, inda ya yi bayanin irin abubuwan da zai yi idan ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Osinbajo a cikin jawabin nasa, ya ce, yana neman tsaya wa takarar ne, domin inganta rayuwar ‘yan ƙasar, yana mai cewa, a matsayinsa na Mataimakin Shugaban Ƙasa yana da ƙwarewar shugabancin Nijeriya.

“A cikin shekara bakwai, na yi wa gwamnati hidima a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin Shugaban Ƙasa, na wakilci gwamanti nan a muhimman ɓangarori a ƙasashen waje. Na ziyarci kusan kafatanin ƙananan hukumomin Nijeriya. Na je kasuwanni da masana’antu da makarantu da gonaki,” inji Osinbajo.

Ya ƙara da cewa, ya je gidajen talakawan ƙasar a yankuna daban-daban, sannan “na tattauna da ƙwararru a ɓangaren fasaha a Legas, Edo da Kaduna da kuma taurarin Nollywood da Kannywood da mawaƙa daga Legas, Onitsha da kuma Kano. Kuma na yi magana da ƙanana da manyan ‘yan kasuwa.”

Osinbanjo ya ce, ya samu wannan ƙwarewa ce, domin ta zama silar fahimtar matsalolon Nijeriya da kuma yadda zai magance su.

Baya ga kewaya da zai yi wa jihohi, domin neman magoya baya, ‘yan kwamitin yaqin neman zaɓensa za su shirya ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a, domin tattara shawarwari game da matakin da ya ɗauka na tsaya wa takarar a zaɓen 2023.

A wata liyafar cin abincin buɗe baki da Osinbanjo ya shirya kuma ya gayyaci sanatocin APC a makon nan, ya bayyana wa sanatocin muradinsa na yin takara da kuma tuntuɓar su, don samun goyon bayansu a kowane yanayi kamar yadda shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana.

“Yana son mu ji daga bakinsa kuma mun ji, kuma yana neman goyon bayanmu a kowanne yanayi da za mu iya. Mun yi wa Mataimakin Shugaban Ƙasan fatan alheri a kan burinsa. 

“Amma bari na tabbatarwa da kowa cewa, sanatocin APC da dukkan ‘yan majalisar tarayya ƙarƙashin APC za su cigaba da aiki tuƙuru wurin ganin cigaban jam’iyyarmu, domin ta cigaba da ayyuka ga ‘yan Nijeriya wurin tabbatar da mulkin APC ne zai cigaba a 2023 har a sauran jihohinmu da izinin Ubangiji APC ne za ta mulke su,” in ji Lawan.

Sai dai kuma, sa’o’i kaɗan bayan Yemi Osinbanjo ya bayyana aniyarsa ta yin takara, sai jagoran jam’iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata magana mai kama da martani ga Farfesa Osinbanjo bayan ganawarsa da gwamnonin APC a gidan Gwamnatin Jihar Kebbi da ke Asokoro a Abuja, don neman goyon bayansu, wanda kuma duniya ta haƙiƙance cewa, Osinbanjo tamkar ɗa ne ga Tinubu a siyasance tun lokacin da yana gwamnan Jihar Legas shi kuma yana kwamishinan shari’a.

Tsohon gwamnnan na Legas ya sake jaddada cewa, yanzu ba shi da buri sama da ganin ya gaje kujerar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a zaven 2023.

Sai dai da wani ɗan jarida ya yi masa tambaya kan matsayarsa ta shiga takara da yaron gidansa, Yemi Osinbajo, ya yi, sai ya amsa da cewa, “shi ba shi da wani ɗa da ya girma da har zai iya karawa da shi.”

Wannan martani na Tinubu kamar yadda masu sharhi ke bayyanawa ya nuna cewa, a na siyasar kowa-tasa-ta-fisshe-shi. Ma’ana; duk wanda ya iya allonsa ya wanke.

Amma idan za a iya tunawa, Bola Tinubu ya sha bayyana yadda ya yi aiki da Yemi Osinbajo a lokacin da shi ya ke gwamna a Legas. Osinbajo ya riqe Kwamishinan Shari’a a lokacin.

Tinubu a lokacin taya Osinbanjo murnar cikarsa shekara 64 a duniya ya bayyana yadda suka yi aiki tare da kuma yin amfani da shari’a wajen cigaban Jihar Legas sa’ilin da Osinbajo ke riqe da muƙamin Kwamishinan Shari’a a jihar.

“Mafi yawan nasarorin da mu ka samu a Kotun Ƙoli su na ɗauke da tambarin Osinbajo,” inji Tinubu.
Haka zalika, Tinubu ya ce, da Osinbajo Gwamnatin Jihar Legas ta

iya karɓo haƙƙoƙinta a gaban kotu.  Tinubu dai a lokacin ya yaba da kishi da riƙe amana da kuma jajircewar Osinbajo da kuma zamansa ɗa mai biyayya a gare shi.

To, sai dai za a iya cewa, waɗancan bayanai ya yi su ne a lokacin da ba a raba gari ba, domin an yi tsammanin cewa, daga yankin Yarabawa, wato Kudu maso Yamma, zai yi wahala wani ya sake fito wa takara matuƙar Tinubu ya fito, saboda tasirinsa da ake gani.

Idan dai za a iya tunawa, shine ɗan jam’iyyar APC kaxai wanda ba shine Shugaban Ƙasa ba, amma shi kansa Shugaba Buharin Tinubu ya ke kira a matsauin Jagoran Jam’iyyar Na Ƙasa, maimakon shi Shugaban Ƙasar da a al’adance aka fi sani da matsayin.

Fitowar Osinbajo ta fito da yadda ta yiwu aka daɗe ana ’yar ƙasa tsakanin Jagora Tinubu da Osinbajo, duk da cewa, Tinubun ne ya kawo Mataimakin Shugaban Ƙasar ya take wa Buhari baya a 2015.

Yadda Tinubu ya fito ya yi kalaman da ke nuni da ya sheganta Osinbajo daga kasancewa ɗansa na siyasa, hakan ya nuna cewa, a na neman shiga ƙazamar siyasar cikin gida, domin baya ga kasancewarsu ’yan Jam’iyyar APC, sun kuma fito daga yankin Kudu maso Yamma, sannan sun fito daga ƙabila guda ta Yarabawa.

Idan a na batun kuɗi da tarin ’yan siyasa, matuƙar aka ambaci Bola Tinubu a siyasar APC za a iya cewa, an ƙure adaka. Haka nan kuma muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa ba ƙaramin muƙami ba ne a siyasar Nijeriya ta yadda zai iya yin matuƙar tasiri wajen fitar da ɗan takara.

Daga dukkan alamu Shugaba Muhammadu Buhari har kawo yanzu bai nuna inda ya karkata ba wajen tsayar da ɗan takara a jam’iyyarsu ta APC. Don haka za a iya cewa, kowa ya iya allonsa, ya wanke.

Yanzu dai an zura idanu a ga yadda za ta kaya tsakanin wannan uba da xa a siyasance. Shin wane ne zai janye wa wani? Idan kuma sasancin bai yiwu ba, sai a zura idanu a ga wanda zai iya kayar da wani? Ko kuwa za a yi mutuwar ragas ne?