Tinubu na ƙoƙarin rage adadin rashin aikin yi a Nijeriya – Shettima

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙarin ganin an samu raguwar adadin rashin aikin yi a tsakanin al’ummar Nijeriya.

Shettima ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da wata takarda game da inganta al’umma da ci-gabansu a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa.

Ya ce, gwamnatinsu ta duƙufa wajen inganta al’ummar Nijeriya ta ɓangarori na zamani daban-daban ta yadda za su riƙe kawunansu a ko’ina suka tsinci kansu a duniya.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce, shirye-shirye da gwamnatin ke yi su na taka muhimmiyar rawa wajen rage adadin marasa ayyukan yi a cikin al’umma ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu.

Har’ilayau, ya Shettima ya ce ya zama wajibi a kawo ƙarshen ababen da ke haifar da koma-baya a cikin al’umma da halin matsi ta su ke ciki, ya na mai cewa shirye-shiryen inganta al’umma za su taimaka gaya wajen cimma haka.