Tinubu na buƙatar addu’a don samun nasarar gudanar da mulki – Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewar zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na buƙatar samun ƙarin addu’o’i daga ‘yan Nijeriya, domin samun damar gudanar da mulki cikin nasara.

Masari ya bayyana haka ne a Fadar Gwamnatin Jihar, lokacin da yake jawabi a wurin taron buɗa-baki wanda aka shirya albarkacin watan Ramadan.

A cewar Masari, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar kan shirya irin wannan taron don yin addu’o’i lokacin watan Ramadan.

Kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN), ya ambato Masari yana cewa, “An shirya taron wannan shekarar domin yin godiya ga Allah kan nasarar da muka samu, lokacin da aka gudanar da manyan zaɓuka a ƙasar nan.

“Babu abin da za mu iya yi face mu gode wa Allah kan nasarar da muka samu a Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.

“Wannan shi ne babban dalilinmu na kasancewa a nan tare da malaman addini, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

“A yanzu shi ne (Tinubu) zai zama sabon shugaban ƙasar Nijeriya, don haka yana buƙatar ƙarin addu’o’i, na gode wa Allah tun da mutane sun fahimci cewar bayan kammala zaɓen shugabanni addu’a ita ce abun da ke biyo baya.” Inji Masari.