Tinubu ne zai bayyana sabuwar ranar da za a yi ƙidayar jama’a – NPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne da kansa zai bayyana sabbin ranakun da za a gudanar da ƙidayar jama’a da gidaje a Nijeriya.

Shugaban hukumar, Nasir Isah Kwarra ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, bayan ya jagoranci tawagar hukumar domin yin bayanin inda suka kwana ga Shugaba Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Ya ce ya zuwa yanzu, hukumar ta miƙa rahotonta ga Shugaban, kuma shi take jira ya yi nazari a kai sannan ya yanke hukunci kan lokacin da za a gudanar da ita.

Sai dai ya ce saboda tsawon lokacin da ake dauka, bukatun hukumar na karuwa, don haka akwai yuwuwar su buƙaci karin kuxi a nan gaba.

Ya ce, “Mun yi masa cikakken bayani a kan shirye-shiryenmu, kuma muna farin ciki Shugaban ya nuna a shirye yake ya tallafa wa dukka tsare-tsarenmu 100 bisa 100 kan dukka buƙatunmu.

“Saboda haka, mu za mu je mu ci gaba da shirye-shiryenmu, kuma za a ji daga bakinsa, ranakun da za a yi ƙidayar a nan gaba, saboda mu mun riga mun mika masa rahoto, zai kuma yi nazari a kai.

“Amma dai ya ba mu tabbacin tallafa mana, kuma muna gode masa a kan haka, musamman la’akari da muhimmancin ƙidaya wajen tsare-tsaren cigaban kasa,” inji Nasiru Kwarra.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *