Tinubu ne zai kai Nijeriya gaba – TAG

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Asiwaju (TAG) ta bayyana tsayawar Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC 2023 a matsayin nasara ga ɗaukacin ’ya’yan jam’iyyar da ma ’yan Nijeriya baki ɗaya.

Ms Oyinkan Okeowo, shugabar gudanar da ayyukan TAG na ƙasa, a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ranar Laraba a Abuja, ta ce, ƙungiyar ta yi farin cikin samun nasarar Tinubu a babban taron jam’iyyar APC na musamman da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa.

Ta ƙara da cewa, idan da Tinubu bai ci zaɓen ba, da abin ya ɓaci, duba da irin ɗimbin goyon bayan da ya ke da shi a faɗin ƙasar nan.

Ta ce, hakan ya faru ne saboda Tinubu ya yi tasiri ga rayuwar ’yan Nijeriya da dama da suke shirye su mara masa baya a zaɓe ko ta halin ƙaƙa.

Okeowo ya bayyana cewa, Tinubu ɗan Nijeriya ne wanda siyasarsa ta kayyade shiyyoyi shida na siyasar ƙasar tare da abokai a faɗin asar da kuma ƙasashen waje.

Ta ƙara da cewa, Tinubu ya yi fice a tsakanin sauran masu neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a 2023 a matsayin wanda ke da ƙirjin yaƙin siyasa don ya fafatawa da Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP.

Ta kuma ba da tabbacin cewa, da Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya a 2023, an tabbatar da kyakkyawar makoma mai kyau ga ɗaukacin ’yan Nijeriya, ba tare da la’akari da addini, ƙabila da siyasa ba, a taƙaice dai, shi mutum ne na kowa.

Ta ce, Tinubu a matsayinsa na tsohon gwamnan jihar Legas da ya yi wa’adi biyu an gwada shi kuma an amince da shi, kuma zai yi fiye da haka a matsayinsa na shugaban ƙasar.

“Siyasa ta wuce kuɗi kawai. Yana da game da samun tsari, tasiri, ƙawance, da kuma tasiri rayuwar mutane da kyau, Tinubu yana da duk wannan a gare shi, ya zuba jari a cikin mutane.

“A matsayinsa na mai rai, dole zai yi kura-kurai, amma abubuwan da ya yi a jihar Legas suna nan don kowa ya gani, ba abubuwa ne voyayyu ba.

“Muna yiwa waɗanda suka janye masa daga takara kuma su ka ba da goyon baya ga fitowarsa, lallai su ’yan kishin dimokaraɗiyya ne, tabbas tarihi zai tuna da su,” inji ta.

NAN ta ruwaito cewa, Tinubu ya kaɗa ƙuri’u 1,271 a babban taron jam’iyyar APC na musamman da kuma zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa domin ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023.

Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani da ƙuri’u 316 yayin da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya zo na uku da 235.