Tinubu ya ƙaddamar da shirin biyan Naira 8,000 ga magidanta miliyan 12

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da wani shiri na biyan Naira 8,000 na tsawon watanni shida ga iyalai miliyan 12 domin magance wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi.

An bayyana hakan ne a cikin wata takarda da Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Tajudeen Abbas ya karanta a Zauren Majalisar a ranar Talata, 11 ga Yuli, 2023.

Tinubu ya ce wannan tallafi ne domin baiwa talakawa da marasa galihu ‘yan Nijeriya damar shawo kan tsadar biyan buƙatu.

Wasiƙar ta kasance ne don amincewa da ƙarin kuɗi don shirin samar da tsaro na zamantakewar jama’a na ƙasa wanda Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta haɓaka.

Ya ce hakan zai yi tasiri mai yawa kan mutane kusan miliyan 60. Domin tabbatar da sahihancin tsarin, ya ce za a yi amfani da zamani kai tsaye zuwa asusun masu cin gajiyar.