Tinubu ya ƙara wa ma’aikatan lafiya waa’adin ritaya zuwa shekaru 65

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya amince da dokar da ke neman ƙarin wa’adi ga ritayar likitoci da masu aikin kiwon lafiya zuwa shekaru 65.

Sakataren yaɗa labarai na Ƙungiyar Harkokin Lafiya ta Ƙasa (NMA), Dakta Mannir Bature ta faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Legas.

Ya ce an umarci Ministan Lafiya da Kula da al’umma, Farfesa Muhammad Pate da ya miƙa buƙatar hakan ga ƙungiyar ta ofishin Shugaban Ma’aikata don zartarwa.

Dakta Bature ya ce Ministan Lafiyar ya gabatar da tsarin a yayin wani zama da Shugaban NMA, Farfesa Bala Audu da manyan masu-ruwa-da-tsaki a harkokin lafiya.

Ya ce ci-gaban ya samu ne la’akari da kula da likitoci da sauran masu harkar kiwon lafiya a Nijeriya.

Ya kuma ce ministan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a fara biyan ma’aikatan lafiya kuɗaɗensu da sabon tsari sakamakon sauye-sauyen da aka samu na sabon tsarin mafi ƙarancin albashi da makamantansa.

Hakan na zuwa ne a ƙoƙarin Gwamnatin Shugaba Tinubu na bunƙasa harkar lafiya da ma’aikatanta a Nijeriya.