Tinubu ya ƙi amincewa da Majalisar Tattalin Arziki kan janye ƙudirin neman yi wa dokar haraji kwaskwarima

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake samun cecekuce game da ƙudirorin da ke neman a yi wa haraji kwaskwarima a Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ba za a janye takardar ƙudirin ba daga Majalisa.

Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce akwai buƙatar ƙudirin ya samu dubawa ta Majalisa.

Majalisar Tattalin Arziƙi ƙarƙashin jagorancin Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ta nemi a janye batun kwaskwarimar tare da neman shawarar masu-ruwa-da-tsaki kafin gabatar da shi.

Shugaba Tinubu ya yaba wa mambobin kwamitin musamman mataimakin nasa da gwamnnoni 36 na jihohin Nijeriya ga shawarar da suka bayar.

Kakakin shugaban ƙasar ya ce a lokacin da Tinubu ya samar da kwamiti kan gyaran tsarin haraji da kasafi a shekarar 2023, burinsa shi ne a inganta harkar tattali ta yadda za a ke gudanar kasuwanci da zuba hannun-jari cikin tsari mai kyau.

Ya kuma tabbatar da cewa kwamitin na aiki tuƙuru a tsawon shekara guda don ganin an cimma kyawawan manufofin da Shugaba Tinubu ya nemi a samar.