Tinubu ya ɗage taron majalisar zartarwa saboda rasuwar Lagbaja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci ɗage taron majalisar zartarwa ta tarayya zuwa wata ranar da za a sanar nan gaba.

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba. Ya ce, “An ɗage taron majalisar ne da aka shirya yi yau domin girmama Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, babban hafsan sojojin ƙasa wanda ya rasu a daren Talata.”

Janar Lagbaja ya yi aiki a matsayin babban hafsan sojojin ƙasa tun ranar 19 ga watan Yuni, 2023, har zuwa rasuwarsa a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024.

Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin a sauke tutoci a duk faɗin ƙasa na tsawon kwana bakwai domin girmama marigayin.

A safiyar Laraba, 6 ga Nuwamba, Shugaban ƙasa ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan Lagbaja da kuma rundunar sojojin Nijeriya. Ya yi addu’ar Allah ya jiƙansa da rahama tare da yabawa da muhimmin gudunmawar da ya bayar wa ƙasa.