Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC, ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta shirya yi, inda ta danganta matakin da Gwamnatin Tarayya qarqashin jagorancin Bola Tinubu ta cimma cika dukkan buƙatunsu.
Da farko dai ƙungiyoyin awadagon sun ƙaddamar da yajin aikin ne sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi, wanda hakan ya haifar da ƙarin farashin man fetur da tsadar rayuwa.
Babban maƙasudin yajin aikin dai shi ne matsawa Gwamnatin Tarayya lamba kan ta sauya ƙarin kashi 200 cikin 100 na farashin man fetur.
Bayan tattaunawa da yawa da suka haɗa da wakilai daga gwamnatin Bola Tinubu, da ƙungiyar awadago ta Nijeriya NLC, da TUC, an dakatar da shirin yajin aikin.
Ɗaya daga cikin muhimman buƙatu da TUC ta gabatar shi ne aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N200,000.
A wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, 06 ga watan Yuni, 2023, Babban Sakataren Ƙungiyar ta TUC, Nuhu Toro, ya bayyana cewa, “Gaskiya a lokacin taruka da tattaunawa da gwamnati, sun amince da dukkan buƙatunmu, saboda haka, babu buƙatar a cigaba da aiwatar da wani mataki na yajin aiki.
“Maƙasudin yajin aikin shi ne don jawo hankalin gwamnati kan buƙatunmu, kuma mun samu nasarar cimma hakan, amma wannan maganar ba ta ƙare ba, za mu sake zama a ranar 19 ga watan Yuni domin tantance halin da ake ciki.