Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a Ribas, ya dakatar da Fubara

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Vice Admiral Ibokette Ibas (mai ritaya) a matsayin mai kula da al’amuran Jihar Ribas, domin ci gaban al’ummar jihar. Tinubu ya sanar da wannan mataki a cikin wata hira da aka yi da shi a faɗin kasa ranar Talata.

Ya ce naɗin ya zama dole domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar, tare da bayyana cewa wannan mataki ba ya shafar ɓangaren shari’a na jihar, wanda zai ci gaba da aiki kamar yadda doka ta tanada.

A cikin jawabinsa, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ya kuma ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas, sakamakon rikicin siyasa da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jihar. Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da ingantaccen gudanar da al’amuran mulki. Shugaban ƙasar ya ce dole ne a ɗauki matakan gaggawa don hana rikicin ya zamo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Bugu da ƙari, Shugaba Tinubu ya sanar da dakatar da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da dukkan ‘yan majalisar dokokin jihar guda 27 na tsawon wata shida. Ya ce dakatarwar ta zama dole domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi na almubazzaranci da rashin ɗa’a a cikin mulkin jihar.

Matakin naɗin Admiral Ibas da kuma dakatar da manyan shugabannin jihar ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’ummar jihar da masu sharhi kan harkokin siyasa.

Wasu na ganin matakin ya dace da ƙoƙarin daƙile rikici da taɓarɓarewar tsaro, yayin da wasu ke ganin ya kamata a bi hanyoyin dimokuradiyya wajen magance rikicin. Sai dai, ana ci gaba da sauraron martani daga ɓangarorin daban-daban kan wannan mataki na shugaban ƙasa.